Yanzu Yanzu: Tsohon Babban Alkalin Jigawa Ringim ya mutu a hatsarin mota

Yanzu Yanzu: Tsohon Babban Alkalin Jigawa Ringim ya mutu a hatsarin mota

- Allah ya yi wa tsohon babban alkalin jihar Jigawa Aminu Sabo Ringim rasuwa

- Sabo Rinim ya rasu ne sakamakon hatsarin mota kauyen Shafar, karamar hukumar Ringim da ke jihar

- Yana tare da dansa a cikin mota lokacin da mummunan al'amarin ya afku, sai dai dan nasa na asibiti yana samun kulawar likitoci

Tsohon babban alkalin jihar Jigawa Aminu Sabo Ringim ya mutu a wani hatsarin mota a kauyen Shafar, karamar hukumar Ringim da ke jihar.

Mista Adamu Shehu, jami'in hulda da jama'a na rundunar tsaro ta farin kaya (NSCDC) na jihar Jigawa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Dutse.

KU KARANTA KUMA: Kyakkyawan hoton tsohon Masallaci a Legas ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta

Yanzu Yanzu: Tsohon Babban Alkalin Jigawa Ringim ya mutu a hatsarin mota
Yanzu Yanzu: Tsohon Babban Alkalin Jigawa Ringim ya mutu a hatsarin mota Hoto: The Nation
Asali: UGC

“Lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:00 na rana. a yau a kauyen Shafar da ke karamar hukumar Ringim bayan mamacin, wanda ke tuka mota kirar Peugeot 206 daga Dutse zuwa Ringim, ya rasa yadda zai yi a kan wata kwana da ta bi ta hanyar Chaichai-Ringim.

"Lamarin ya cika da mutane biyu, tsohon Babban Alkalin da dansa," in ji Shehu.

Ya ce an garzaya da dukkan wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Ringim inda aka tabbatar da tsohon babban alkalin ya mutu, jaridar The Nation ta ruwaito.

Jaridar Daily Post ta kuma ruwaito cewa kakakin NSCDC din ya ce, dan marigayin, wanda ya samu rauni daban-daban a halin yanzu yana samun kulawar likita a asibiti.

KU KARANTA KUMA: Aminu Dantata ya cika shekaru 90: Ga wani balli daga cikin tarihinsa

Lokacin da aka tuntubi kakakin ma’aikatar shari’ar jihar, Hajiya Zainab Baba-Santali, ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta yi alkawarin bayar da sanarwa nan ba da jimawa ba.

Ta ce: "Ma’aikatar za ta fitar da sanarwa dangane da marigayin, da zaran Kwamishinan Shari’a na Jihar kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Dokta Musa Adamu ya dawo daga binne shi."

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Allah yayi wa tsohon shugaban ma'aikatan tsaro, Laftanal Janar Joshua Dogonyaro rasuwa. Dogonyaro yayi aiki ne zamanin mulkin tsohon shugaban kasa marigayi Janar Sani Abacha.

Joshua Dogonyaro ya rasu yana da shekaru 80 cif a duniya. Majiyoyi daga iyalansa sun tabbatar da cewa ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Jos a sa'o'in farko na ranar Alhamis, 13 ga watan Mayun 2021.

Tuni da aka mika gawar marigayin ma'adanar gawawwaki dake asibitin sojoji na Jos, jihar Filato, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel