Kyakkyawan hoton tsohon Masallaci a Legas ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta

Kyakkyawan hoton tsohon Masallaci a Legas ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta

- Hoton tsohon masallaci a Legas ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu a shafukan sada zumunta bayan da aka wallafa shi a shafin Twitter

- Wani dan kasar Saliyo haifaffen Najeriya, Mohammed Shitta ne ya kafa masallacin a 1892

- 'Yan Najeriya a shafukan sada zumunta sun yi mamakin yadda tsohon gini kamar haka yake tsaye har yanzu yayin da gine-ginen zamani suka ruguje

A kwanan nan ne aka wallafa hoton tsohon masallaci a Legas, Masallacin Shitta-Bey, a shafin soshiyal midita na gwamnatin jihar.

Da yake wallafa hoton a Twitter, shafin @followlasg ya bayyana cewa masallacin, wanda aka gina a 1892, yana daya daga cikin masallatai mafi tsufa a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Aminu Dantata ya cika shekaru 90: Ga wani balli daga cikin tarihinsa

Kyakkyawan hoton tsohon Masallaci a Legas ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta
Kyakkyawan hoton tsohon Masallaci a Legas ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta Hoto: @followlasg
Asali: Twitter

A shekarar 2013, Hukumar Kula da Gidajen adana kayayyakin tarihi ta sanya masallacin a matsayin wani abin tarihi na kasa.

Masallacin wanda wani dan asalin kasar Saliyo haifaffen Najeriya, Mohammed Shitta ya kafa, ana daukar sa a matsayin daya daga cikin muhimman kayayyakin tarihin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: 2023: Hotunan Neman Takarar Sanata na Gwamna Ortom Sun Mamaye Makurdi

Da ya je sashen sharhi na wallafar, @Wale_Bello ya ce:

"Wannan masallacin har yanzu yana da tsari mai karfi bayan sama da shekaru 128. Mutum zai yi mamakin dalilin da yasa tsarin zamani ba ya karko kamar irin wannan."

@aabitaj70 ya rubuta:

"Cin hanci da rashawa."

@coolMuhman ya ce:

"Kenan an shigo da Musulunci cikin Nijeriya a shekarar 1892? Haba baka darajamu ba ko kadan? A Arewa an gabatar da addinin musulunci sama da shekaru 500 kafin ginin wannan masallacin to ta yaya zai zama mafi dadewa?"

Da yake mayar da martani ga @coolMuhman, @phemnahs ya yi tsokaci:

"Wataƙila ya kamata ku natsu ka sake karanta rubutun. A wannan karon, a hankali !!!"

A wani labarin, wani dan Najeriya mai suna Ayo Ojeniyi ya wallafa hotunan gidan marigayi Obafemi Awolowo a shafinsa na Facebook.

Awolowo mutum ne mai kishin kasa kuma shine firemiyan farko na yankin yammacin kasar nan. An haifeshi a ranar 6 ga watan Maris 1909 kuma ya rasu a ranar 9 ga watan Mayun 1987.

Ga hotunan da Ojeniyi ya wallafa tare da tambayar: "Yaushe rabonku da ziyartar gidan Awolowo dake Ikenne?"

Asali: Legit.ng

Online view pixel