Da Ɗumi Ɗumi: Ba Wani Sabon Bashi Shugaba Buhari Zai Karɓo Ba, Majalisa Tayi Ƙarin Haske

Da Ɗumi Ɗumi: Ba Wani Sabon Bashi Shugaba Buhari Zai Karɓo Ba, Majalisa Tayi Ƙarin Haske

- Yan majalisar dattijai sun yi cikakken bayani kan abinda ke ƙunshe a takardar da shugaba Buhari ya aike musu jiya Talata

- Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Yahaya Abdullahi yace ba wani sabon bashi shugaba buhari zai karɓo ba

- Yace wannan bashin an riga anyi maganarsa tun sanda shugaban ya turo da kasafin kuɗin wannan shekarar

Yan majalisar dattijai sun yi bayani game da wasiƙar da shugaba Buhari ya aike musu a zaman su na jiya Talata.

KARANTA ANAN: Matsalar Tsaro: Zamu Yi Amfani da Dukkan Ƙarfin Mu Wajen Taimaka Wa Najeriya, Shugaban Faransa

A wasiƙar da shugaban ya aike musu ya nemi sahalewar su ya karɓo rancen kuɗi kimanin Naira 2.3 tiriliyan don cike gurbin kasafin kuɗi na wannan shekarar.

Da Ɗumi Ɗumi: Ba Wani Sabon Bashi Shugaba Buhari Zai Karɓo Ba, Majalisa Tayi Ƙarin Haske
Da Ɗumi Ɗumi: Ba Wani Sabon Bashi Shugaba Buhari Zai Karɓo Ba, Majalisa Tayi Ƙarin Haske Hoto: @NGRsenate
Asali: Twitter

Bayan karanta wannan wasiƙa a zauren majalisar jiya Talata, labarin rancen ya karaɗe ko ina kafafaen sada zumunta, inda wasu yan Najeriya suka fara sukar shugaban.

KARANTA ANAN: Rundunar Soji Ta Riƙe Albashin Sojoji 45 a Jihar Borno Saboda Wani Zargi

Amma shugaban masu rinjaye na majalisar dattijan Najeriya, Sanata Yahaya Abdullahi, yayi ƙarin haske kan wasikar a wata hira da yayi da BBC ta wayar salula.

Sanatan yace:

"Mutane basu fahimci ainihin abinda takardar ke nufi ba, ba wani sabon bashi shugaban Ƙasa Buhari zai karɓo ba, daman can akwai maganar wannan bashin na 2.3 triliyan."

"Amincewar majalisa kawai yake nema don cika sharuɗɗan karɓo rance, wanda aka yi maganarsa tun sanda shugaban ya turo da kasafin kuɗin wannan shekarar."

A wani labarin kuma Yan Bindiga Su Hallaka Sojoji Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Wani Ɗan China

A ranar Litinin, wasu yan bindiga sun kashe jami'an soji biyu tare da sace wani ɗan China a ƙaramar hukumar Magama jihar Neja.

Jami'an soji sun maida martani ga yan bindigan inda akai ɗauki ba daɗi a tsakaninsu, biyu daga cikin sojojin sun rasa rayuwarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262