Da duminsa: Tsohon shugaban ma'aikatan tsaro na Najeriya ya rasu

Da duminsa: Tsohon shugaban ma'aikatan tsaro na Najeriya ya rasu

- A ranar Alhamis, 13 ga watan Mayun 2021 ne rundunar sojin Najeriya ta samu labari mara dadi

- Tsohon shugaban ma'aikatan tsaro na kasa, Laftanal Janar Joshua Dogonyaro ya rasu da safe

- Dogonyaro ya rasu ne sakamakon rashin lafiyan da yayi a wani asibiti a Filato kuma yana da shekaru 80

Allah yayi wa tsohon shugaban ma'aikatan tsaro, Laftanal Janar Joshua Dogonyaro rasuwa. Dogonyaro yayi aiki ne zamanin mulkin tsohon shugaban kasa marigayi Janar Sani Abacha.

Joshua Dogonyaro ya rasu yana da shekaru 80 cif a duniya. Majiyoyi daga iyalansa sun tabbatar da cewa ya rasu ne a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Jos a sa'o'in farko na ranar Alhamis, 13 ga watan Mayun 2021.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke 'yan bindiga 4, sun kwato shanu 170 a Katsina

Da duminsa: Tsohon shugaban ma'aikatan tsaro na Najeriya ya rasu
Da duminsa: Tsohon shugaban ma'aikatan tsaro na Najeriya ya rasu. Hoto daga tribuneonlineng.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Boko Haram: Majalisar tarayya ta bukaci duba ababen hawa da kyau kafin shigarsu ciki

Tuni da aka mika gawar marigayin ma'adanar gawawwaki dake asibitin sojoji na Jos, jihar Filato, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Manjo Gabriel Adofiku mai ritaya tsohon jami'in Dogonyaro, ya sanar da manema labarai cewa tsohon shugaban ma'aikatan tsaron ya rasu ne wurin karfe 3:30 na asuba.

An haifa Dogonyaro a ranar 12 ga watan Satumban 1940 a garin Vom dake jihar Filato.

Ya halarci makarantar sakandare ta maza dake Gindiri, ya halarci makarantar horar da hafsin soji dake Kaduna daga 1964 zuwa 1967, ya halarci makarantar horar da soji dake Jaji, yayi kwasa-kwasa a Amurka da Ingila.

A wani labari na daban, Ali Ndume, sanata mai wakiltar mazabar Borno ta kudu a majalisar dattawa, ya soki hukuncin gwamnonin kudu na haramta kiwo a bude tare da hana yawon shanu a kasa.

Gwamnonin sun yanke wannan hukuncin ne a wani taro da suka yi a jihar Delta a ranar Talata. Kamar yadda suka ce, haramta kiwon zai hana fadace-fadacen da ake yawan samu tsakanin manoma da makiyaya kuma hakan zai inganta tsaron yankin, The Cable ta ruwaito.

Amma a yayin jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba, Ndume yace gwamnonin sun fara neman dorawa wasu laifi a yayin shawo kan matsalarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel