Da dumi-dumi: NECO ta dage jarrabawar neman gurbin shiga makarantun sakandare
- Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta dage gudanar da jarabawar neman gurbin shiga makrantun sakandare na 2021
- An dage jarrabawar zuwa ranar Asabar 5 ga watan Yuni sabanin 29 ga watan Mayu da ta tsara da farko
- Hakan ya kasance ne domin ba wa jihohin da ke da karancin dalibai damar yin rajista
Hukumar shirya Jarrabawar kammala sakandire ta kasa (NECO) ta dage gudanar da Jarrabawar kammala firamare wato Common entrance ta shekarar 2021, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A cewar shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NECO, Mista Azeez Sani, an dage jarrabawar zuwa ranar 5 ga watan Yuni.
KU KARANTA KUMA: Kyakkyawan hoton tsohon Masallaci a Legas ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kakakin hukumar ya ce, alkaluman wadanda suka yi rijistan jarrabawar ya zuwa yanzu bai kai yadda ake tsammani ba. NECO, duk da haka, yana fatan cewa tsawaita mako guda zai ba da dama ga ƙarin dalibai.
Sani ya ce “An daga jarabawar da aka tsara gudanarwa ranar 29 ga Mayu, 2021 ne, domin ba wa jihohin da ke da karancin dalibai damar yin rajista.
“Ana kuma sanar da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki da su lura da sauyin.”
Hukumar ta kara da cewa za a ci gaba a yin rajistar daliban da ke son yin jarabwar har zuwa ranar da za rubuta jarabawar.
KU KARANTA KUMA: Aminu Dantata ya cika shekaru 90: Ga wani balli daga cikin tarihinsa
Sanawar ta shawarci dalibai da su sauke jadawalin jarabawar daga shafin hukumar na: www.neco.gov.ng.
A wani laarin, Gwamnatin jihar Kano ta fara daukar matakai na daukar likitoci 56 tare da gudanar da gwaje-gwaje na kwarewa ga wadanda aka zaba.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, jihar ta ce hakan zai bunkasa ayyukan sashen lafiya na matakin farko.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mista Maikudi Marafa, jami'in hulda da jama'a na hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar ya sanya wa hannu a ranar Talata.
Asali: Legit.ng