Gwamnatin Ganduje Za Ta Kara Daukar Likitoci Aiki a Jihar Kano

Gwamnatin Ganduje Za Ta Kara Daukar Likitoci Aiki a Jihar Kano

- Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa, tana shirye-shiryen daukar likitoci sama da 50 aiki

- Tuni hukumar da ke da alhalin tantance daukar aikin ta fara gudanar da ayyukan da suka dace

- An ruwaito cewa, za a dauki likitocin ne saboda su yi aiki a hukumar kula da lafiya a matakin farko

Gwamnatin jihar Kano ta fara daukar matakai na daukar likitoci 56 tare da gudanar da gwaje-gwaje na kwarewa ga wadanda aka zaba.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, jihar ta ce hakan zai bunkasa ayyukan sashen lafiya na matakin farko.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mista Maikudi Marafa, jami'in hulda da jama'a na hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar ya sanya wa hannu a ranar Talata.

KU KARANTA: Giyar Mulki Ke Bugar El-Rufai, Za Mu Iya Kulle Najeriya Baki Daya Idan Bai Kula Ba, NUPENG

Gwamnatin Ganduje Za Ta Dauki Karin Likitoci a Jihar Kano
Gwamnatin Ganduje Za Ta Dauki Karin Likitoci a Jihar Kano Hoto: onlinenewsngr.com
Asali: UGC

Ya ce, a cikin sanarwar hukumar ta shawarci masu neman aikin da su kasance cikin shirin tunkarar kalubalen da ke gabansu.

”Sakataren zartarwa na kwamitin, Dr. Tijjani Hussain, ya bukaci masu neman aikin su shirya kan kalubale.”

A cewarsa, za a horar da wadanda suka yi nasarar a bangaren jagoranci, sarrafa bayanai da kuma harkokin kiwon lafiya daban-daban, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Don haka, ya umarce su da su jajirce tare da sadaukar da kai lokacin da suka samu nasara a matsayinsu na ma'aikatan Hukumar Kula da Kiwon Lafiya a matakin farko.

KU KARANTA: Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bayyana Ka'idojin Da Ake Bi Wajen Nada Khalifa a Tijjaniyya

A wani labarin, Jihar Kaduna, musamman ma babban birninta ta ga mummunan yanayin kulle a ranar Litinin yayin da kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ke zanga-zangar korar ma'aikata da gwamnatin jihar ta yi.

Akwai fargabar cewa, zanga-zangar ta shafi harkokin sufuri, kudade da bangarorin wutar lantarki wanda kan iya shafar tattalin arzikin jihar da ake ganin yana daga cikin manyan masu taka rawar gani a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar wani rahoton kididdiga da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) da ta fitar a shekarar 2019, ya zuwa shekarar 2017, Kaduna tana da wani Babban GDP na Naira tiriliyan 2.69 kuma itace matsayin na 10 a jerin jihohi masu karfin tattalin arziki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel