Fadar shugaban kasa ta bankado yunkurin sakin bayanan bogi kan lafiyar kwakwalwar Buhari

Fadar shugaban kasa ta bankado yunkurin sakin bayanan bogi kan lafiyar kwakwalwar Buhari

- Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu, yace wasu mutane sun sha alwashin kai gwamnatin Buhari kasa

- Ministan yace gwamnatin tarayya ta bankado wasu jaridun yanar gizo 476 masu fitar da bayanan bogi kan gwamnati

- Babban lamarin shine yadda ake kokarin fitar da bayanin bogi kan lafiyar kwakwalwar shugaban kasa Muhammadu Buhari

Gwamnatin tarayya tace ta bankado jaridu 476 na yanar gizo da suka sadaukar da ayyukansu kowacce rana wurin fitar da labaran bogi na yaki da gwamnati.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya sanar da hakan a ranar Litinin, 17 ga watan Mayu a Abuja yayin da ya karba bakuncin jami'an NIPR da suka ziyarcesa.

Legit.ng ta tattaro cewa Mohammed ya ce babban abun bada mamakin da aka bankado shine yadda ake kokarin fitar da bayanin bogi kan lafiyar kwakwalwar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Allah yayi wa zukekiyar jarumar Kannywood, Khadija Mahmud, rasuwa

Fadar shugaban kasa ta bankado yunkurin sakin bayanan bogi kan lafiyar kwakwalwar Buhari
Fadar shugaban kasa ta bankado yunkurin sakin bayanan bogi kan lafiyar kwakwalwar Buhari. Hoto daga @TheCableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yajin aikin ma'aikatan Kaduna: Mun shirya muku, El-Rufai ga NLC, PDP

Ya ce: "Za ku sha mamaki idan nace muku cikin kwanakin nan mun bankado jaridun yanar gizo 476 da suka sadaukar da ayyukansu wurin yada labaran bogi kan gwamnati.

"Na kwanan nan kuma babban abun mamakin shine wanda suka ce a zuwan Buhari Ingila na kwanakin baya, likitoci sun bakacesa da ya yi murabus saboda baya iya ko gane iyalansa.

"Na fara tunanin ta yaya zasu kai har nan, ko kuma saboda sun san mutane na sauraronsu ne kuma dole sai sun yada labaran bogi."

A wani labari na daban, dakatacciyar shugaban hukumar NPA, Hadiza Bala Usman ta yi martani da tsohuwar mamba a hukumar, Sanata Binta Garba wacce ta zargeta da waddaka da kudaden hukumar.

Garba ta zargi Usman da assasa korarta daga hukumar NPA a kan yadda ta nuna rashin amincewarta da rahotannin shige da ficen kudade.

A yayin martani, dakatacciyar shugaban NPA a wata takarda da ta sa hannu a ranar Litinin, ta musanta zargin da Garba ke yi mata inda tace Sanatan ta je hukumar ne domin daidaita ta ba wai kawo cigaba ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel