Ku baiwa kanka kariya daga miyagun 'yan bindiga, Ortom ga jama'ar Binuwai

Ku baiwa kanka kariya daga miyagun 'yan bindiga, Ortom ga jama'ar Binuwai

- Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, yayi kira ga 'yan jiharsa da su baiwa kansu kariya daga 'yan bindiga

- Gwamnan wanda ya bayyana a fusace da halin da jiharsa ke ciki, yace ko baka da makami ka shiga makwabta ka aro

- Ya jaddada cewa babu yadda za a yi mutum na cikin gidansa a shiga a kashe shi kamar kiyashi, don haka maza da mata su mike

Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai a ranar Litinin yayi kira ga mazauna jihar da su kare kansu daga miyagun 'yan bindigan dake kutse suna kai masu hari.

Ortom ya sanar da hakan ne yayin martani ga tambayan manema labarai bayan isarsa Makurdi daga jihar Oyo inda ya halarci taron gwamnonin PDP, ya ce akwai bukatar jama'a su mike tsaye domin baiwa gidajensu kariya.

"Na sanar da jama'a da su baiwa kansu kariya. Ba za ku zauna a gidajenku ba kawai wasu su shigo su kashe ku.

"Idan baku da makamai da shari'a ta aminta ku mallaka, ku je makwabta ku nemo. Kowanne mutum dake Binuwai, mata da maza, ku baiwa kanku kariya," yace.

KU KARANTA: Jonathan: Ban taba amfani da matsayina wurin musgunawa wani ba ko azabtarwa ba

Ku baiwa kanka kariya daga miyagun 'yan bindiga, Ortom ga jama'ar Binuwai
Ku baiwa kanka kariya daga miyagun 'yan bindiga, Ortom ga jama'ar Binuwai. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hoton mutum 2 suna yi wa Sanusi II sujada ya janyo cece-kuce, tsohon basaraken ya magantu

Gwamnan wanda a bayyane fusace yake da sabbin kashe-kashen da ake zargin makiyaya ne ke yi a sassan jihar, ya jaddada cewa lokaci yayi da jama'a zasu baiwa kansu kariya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A yayin tsokaci a kan taron gwamnonin, ya bayyana cewa kungiyar ta shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya baiwa matsalar tsaron kasar nan hankalinsa gaba daya.

"Mu gwamnonin PDP mu kara bayyana goyon bayanmu ga hukuncin gwamnoni kudu na haramta kiwon dabbobi. Muna fatan zamu hada kai da shugaban kasa wurin magance wannan matsalar. Babu yadda za a yi mu aiwatar da hakan ba tare da shugaban kasa ba saboda shine mai karfin iko. Dole ne mu yi aikin tare da shugaban kasa," Ortom yace.

A wani labari na daban, kafin fara yajin aikin kwanaki biyar na jan kunne da kungiyar kwadago ta Najeriya ta shirya farawa a ranar Litinin a jihar Kaduna, Gwamna Nasir El-Rufai yace ya shirya kuma yana jiran shugabannin kungiyar kwadagon da na jam'iyyar adawa ta PDP.

Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar rarrabe wutar lantarki ta Najeriya ta fada yajin aikin tun tsakar daren Asabar kuma ta tsinke dukkan layikanta da suke hade da jihar, lamarin da ya bar jama'ar jihar cikin duhu.

Wannan ya biyo bayan jan kunnen da kungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta kasa ta yi kuma ta bayyana cewa zata bi ayarin NLC wurin tafiya yajin aikin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel