Tashin hankali: Hadimar gwamna ta yanke jiki ta fadi a ofishinta, ta mutu a take
- Farfesa Francisca Aladejana, mai baiwa Gwamna Fayemi shawara ta musamman ta rasu
- An gano cewa Aladejana tayi numfashinta na karshe ne a ranar Litinin, 17 ga watan Mayun 2021
- Ta rasu ne bayan isar ta ofis tana amsa waya amma sai ta yanke jiki ta fadi, a take tace ga garinku
Wani rahoto da jaridar Leadership ta fitar ya bayyana cewa mai baiwa Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti shawara ta musamman a fannin ilimi, Farfesa Francisca Aladejana ta rasu.
Legit.ng ta tattaro cewa, Aladejana wacce ita ce tsohuwar shugaban kwalejin ilimi dake Ikere, jihar Ekiti, ta rasu ne a ranar Litinin, 17 ga wata Mayun 2021.
Kamar koyaushe, mamaciyar ta isa ofishinta da safiyar Litinin amma sai ta yanke jiki ta fadi yayin da take amsa waya.
Kamar yadda rahoto ya bayyana, marigayiyar farfesan 'yar asalin garin Ado Ekiti ita ce tsohuwar shugabar hukumar SUBEB ta jihar Ekiti.
KU KARANTA: Allah yayi wa zukekiyar jarumar Kannywood, Khadija Mahmud, rasuwa
KU KARANTA: Yajin aikin ma'aikatan Kaduna: Mun shirya muku, El-Rufai ga NLC, PDP
A wani labari na daban, majalisar wakilan Najeriya ta shirya tsaf domin halasta amfani da wiwi a kasar nan.
Mai magana da yawun majalisar wakilai, Hon. Benjamin Okezie Kalu ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da yayi jawabi kan amfani da damammakin da za a samu daga tabar wiwi a garin Akure, babban birnin jihar Ondo.
Kalu ya ce majalisar ta shirya tsaf domin shirya taron kwana biyu da masu ruwa da tsaki a kan amfanin wiwi, Vanguard ta ruwaito.
Kamar yadda yace, ranar taron ita ce 7 da 8 ga watan Yuli kuma za a samu masana kimiyya, ma'aikatan lafiya, masu hada magunguna, manoma, kamfanonin inshora da kuma kamfanoni masu zaman kansu da za a yi taron dasu.
Yayi bayanin cewa kasashe irinsu Afrika ta kudu da sauransu a yanzu suna morewa sakamakon noman wiwi da suke yi kuma suna fitar da ita kasashen ketare.
"An kwatanta Najeriya da kasa da ta dogara da mai ba wai kasa mai man fetur ba. A gaskiya dole ne mu kara samo hanyoyin kudin shiga tunda mun san dogaro da mai ba mai yuwuwa bane."
Asali: Legit.ng