Giyar Mulki Ke Bugar El-Rufai, Za Mu Iya Kulle Najeriya Baki Daya Idan Bai Kula Ba, NUPENG

Giyar Mulki Ke Bugar El-Rufai, Za Mu Iya Kulle Najeriya Baki Daya Idan Bai Kula Ba, NUPENG

- Kungiyar NUPENG ta yi gargadin tsundumawa yajin aiki idan ba a dakatar girman kan El-Rufai ba

- Kungiyar ta ce geamnatin tarayya ta gaggauta daukar mataki kan gwamnan na jihar Kaduna kafin lokaci ya kure

- Hakazalika ta yi gargadi ga gwamnan kan cewa, kada a muzanta ko daya daga cikin mambobin kwadago

Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas (NUPENG) ta hannun shugabanta na kasa Kwamared Williams Akporeha sakatarenta Kwamared Afolabi Olawale, ta yi barazanar kulle Najeriya saboda “girman kan” Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Shugabannin kungiyar a cikin wata sanarwa sun ce NUPENG ta yi matukar bakin ciki game da tashin hankalin da ya faru yayin da kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ke zanga-zangar lumana ta “mulkin kama-karya da danniya na Gwamna Nasir El-Rufai a Jihar Kaduna.”

KU KARANTA: Tsohon Sarkin Kano Sanusi Alheri Ne Ga Najeriya, Inji Shugabannin Tijjaniyya

Giyar Mulki Ke Rudar El-Rufai, Za Mu Iya Kulle Najeriya Baki Daya, NUPENG
Giyar Mulki Ke Rudar El-Rufai, Za Mu Iya Kulle Najeriya Baki Daya, NUPENG Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi kira ga El-Rufai ba tare da bata lokaci ba don dakatar dashi "kafin girman kai da giyar mulki sukara sanya lamarin cikin mummunan bala'i kamar yadda yake yi a cikin dukkan batutuwan da suka shafi rayuwar dan adam da jin dadi".

A yayin zanga-zangar ta kwanaki 5 cikin lumana a fadin Jihar, NUPENG ta yi gargadin cewa babu wani shugaban kwadago ko ma’aikata da za a kaiwa hari, tursasa nakasa, wulakanta, ko cin zarafinsu, The Gazette Nigeria ta ruwaito.

Kungiyar ta gargadi gwamnan kan sanya rayukan shugabannin kungiyoyin kwadagon cikin hadari. Ta na mai cewa, idan aka cutar da daya daga cikin shugabanni ko mambobin kwadagon, NEPENG za ta kira dukkan mambobinta a kasar su tsunduma yaji.

"Dangane da abin da ke sama, saboda haka muna sanya dukkan mambobin NUPENG a duk fadin kasar a kan jan kunne kuma a takaice cikin sanarwa na awanni biyar za a yi kira da a dauki matakin masana'antu a duk fadin kasar idan bukatar hakan ya taso."

KU KARANTA: Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bayyana Ka'idojin Da Ake Bi Wajen Nada Khalifa a Tijjaniyya

A wani labarin, Jihar Kaduna, musamman ma babban birninta ta ga mummunan yanayin kulle a ranar Litinin yayin da kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ke zanga-zangar korar ma'aikata da gwamnatin jihar ta yi.

Akwai fargabar cewa, zanga-zangar ta shafi harkokin sufuri, kudade da bangarorin wutar lantarki wanda kan iya shafar tattalin arzikin jihar da ake ganin yana daga cikin manyan masu taka rawar gani a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar wani rahoton kididdiga da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) da ta fitar a shekarar 2019, ya zuwa shekarar 2017, Kaduna tana da wani Babban GDP na Naira tiriliyan 2.69 kuma itace matsayin na 10 a jerin jihohi masu karfin tattalin arziki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel