Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bayyana Ka'idojin Da Ake Bi Wajen Nada Khalifa a Tijjaniyya

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bayyana Ka'idojin Da Ake Bi Wajen Nada Khalifa a Tijjaniyya

- Shararren malamin addanin Islama Shehu Dahiru Bauchi ya bayyana yadda ake nada Khalifa

- Shehin ya bayyana wasu hanyoyi uku da ake bi wajen nada sabon Khalifa a darikar Tijjaniyya

- Shehin ya kuma taya tsohon Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi II da zama Khalifan Tijjaniyya

Shararren Malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya ce akwai matakai uku da ake bi wajen nada Khalifan Darikar Tijjaniyya.

Shehin ya bayyana hakan bayan da ya tarbi Sarkin Kano kuma Khalifan Tijjaniya a Najeriya, Muhammadu Sanusi na II ranar Litinin a gidansa da ke Bauchi.

Shehin ya bayyana hanyoyi uku da ake bi wajen nada Khalifa a darikar Tijjaniyya kamar haka:

1. Wadanda Sheikh Ibrahim Inyass yake nadawa da kansa

2. Wadanda suka gaji wadanda Sheikh Inyass ya nada

3. Wadanda Shehunan darikar Tijjaniyya ta nada

KU KARANTA: Rahoto: Asarar Tiriliyoyi Da Gwamnatin Kaduna ta Tafka Yayin Zanga-Zangar NLC

Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bayyana Ka'idojin Da Ake Bi Wajen Nada Khalifa
Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bayyana Ka'idojin Da Ake Bi Wajen Nada Khalifa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana cewa, nadin Sarki Muhammadu Sanusi ya fada a mataki na uku a cewar Shehun na Bauchi.

Tun da farko, kafin ya gabatar da jawabinsa, Shehin ya bukaci da a karanta masa takardar da shi sabon Khalifan, Muhammadu Sanusi, ya zo da ita daga Kaulaha.

Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa bayan da aka karanta takardar, a cikin jawabinsa ya ce: “Ina taya ka (Sarki Muhammadu Sanusi II) murna, na samun wannan takarda da wannan mukami na Khalifanci.

“Kuma muna maraba da wannan Babban Bako wanda nan gidansu…,” inji Shehin.

A cewarsa, asalin Khalifanci Sheikh Ibrahim Inyass ya bai wa Sarkin Kano Sanusi na I ya faru ne bayan an cire Sarkin daga sarauta.

“Wata rana mun je Makka, sai Shehu Ibrahim yana tambaya na labarin Najeriya ina ba shi har muka iso kan labarin Khalifa Muhammadu Sanusi I.

“Na ce masa an sauke shi daga sarautar Kano inda ya koma Azare… Sai Shehu ya ce tunda mutanen duniya sun raba shi da jama’a, sai Shehu ya hada shi da mutanensa.

“Ya aike ni na je na fadawa mukaddaman Kano musamman Shehu Tijjani.

“Na tara Shehunan Kano na fada musu cewa Shehu ya nada mana Khalifa bayan na fadawa Shehu Tijjani da sauransu.

“Da shekara ta kewayo Shehu ya aiko da takarda a rubuce ta nadin,” inji Shehu Dahiru.

KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: An Dawo da £4.2m Zuwa Najeriya, Kudaden Da Ibori Ya Sace

A wani labarin, Shugabannin darikar Tijjaniyya sun bayyana zaman tsohon Sarkin Kano, Mohammadu Sanusi II shugaban Tijjaniya alheri ga Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Malaman da suka bayyana hakan lokacin da suka kai ziyarar ban girma gidansa na Kaduna sun kuma ce duk mabiyansu a Najeriya da Afirka suna alfahari da shi.

Wakilin shugaban darikar Tijjaniyya na duniya, Sheikh Abdul-Ahad Nyass wanda ya jinjinawa tsohon sarkin ya ce shawara ce ta bai daya da kasancewar tsohon sarki sanusi a matsayin Khalifa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel