Rahoto: Asarar Tiriliyoyi Da Gwamnatin Kaduna ta Tafka Yayin Zanga-Zangar NLC

Rahoto: Asarar Tiriliyoyi Da Gwamnatin Kaduna ta Tafka Yayin Zanga-Zangar NLC

- Rahoton masana tattalin arziki ya bayyana irin asarar da gwamnatin jihar Kaduna ta tafka a kwanaki biyu kacal

- An kirga asarar ne duba da yadda jihar ke samar da kudaden shiga ta fannoni da dama daga cikin jihar

- Hakazalika, an kididdiga yadda zanga-zangar ta NLC ta gurgunta bangarorin kasuwanci da kudin shigan jihar

Jihar Kaduna, musamman ma babban birninta ta ga mummunan yanayin kulle a ranar Litinin yayin da kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ke zanga-zangar korar ma'aikata da gwamnatin jihar ta yi.

Akwai fargabar cewa, zanga-zangar ta shafi harkokin sufuri, kudade da bangarorin wutar lantarki wanda kan iya shafar tattalin arzikin jihar da ake ganin yana daga cikin manyan masu taka rawar gani a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar wani rahoton kididdiga da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) da ta fitar a shekarar 2019, ya zuwa shekarar 2017, Kaduna tana da wani Babban GDP na Naira tiriliyan 2.69 kuma itace matsayin na 10 a jerin jihohi masu karfin tattalin arziki a Najeriya.

Ayyuka da noma sun mamaye GDP da N1.37tr. Sai dai, wadannan fannoni sun kasance cikin mafi munin lalacewa a jiya bio bayan kullen zanga-zangar da ya zama gama gari tun ranar Lahadi.

KU KARANTA: Rikici Ya Barke Tsakanin 'Yan Bindiga Sun Yi Musayar Wuta, Sun Hallaka Junansu a Neja

Rahoto: Asarar Da Gwamnatin Jihar Kaduna ta Tafka Saboda Zanga-Zangar NLC
Rahoto: Asarar Da Gwamnatin Jihar Kaduna ta Tafka Saboda Zanga-Zangar NLC Hoto: truthng.com
Asali: UGC

Dangane da rahoton 2020 na Kungiyar Kasuwanci ta Oxford, tun daga 2015, jihar ta jawo hankalin saka hannun jari sama da dala miliyan 800. A halin yanzu, kamfanoni sun himmatu wajen saka hannun jari kusan dala biliyan 2.1 a cikin shekaru biyu masu zuwa.

Dangane da IGR, rahoton kungiyar kasuwanci na Oxford ya nakalto Gwamna Nasir el-Rufai yana cewa jihar ta ninka IGR din ta daga N13bn a 2015 zuwa N26bn a 2017. Ya kara hauhawa zuwa N44bn a haraji a 2019 bayan saukaka aikin haraji ta hanyar dokoki.

An gano cewa wasu masana’antun da ke wajen garin zanga-zangar ba ta shafe su ba. Gonar Olam da ke gefen titin Kaduna zuwa Abuja zanga-zangar bata shafe ta ba kamar yadda ma’aikatansa ke ofishin tun jiya bayan hutun Sallah

"Muna sane da halin da ake ciki amma kun san ba a tsakiyar gari muke ba, don haka bana tunanin muna bukatar mu damu kanmu a yanzu," in ji wani babban jami'i gonar.

Tuni an tafka asarar Biliyoyi

A halin yanzu, masana sun ce za a yi asarar biliyoyin nairori saboda toshe harkokin kasuwanci a jihar.

Wani tsohon ma’aikacin banki kuma masanin tattalin arziki ya ce da an kauce wa yajin aikin idan da gwamnan jihar ya tattauna da kungiyoyin kwadagon.

“Ana jigilar kaya zuwa arewa ta cikin Kaduna daga arewa ta Kaduna zuwa wasu sassan Najeriya.

"Ku yi tunanin asarar da aka yi saboda katsewar wutar lantarki, kayan aiki, sufuri da sauransu. Ya gudana cikin biliyoyi, ku yi tunanin asibitoci, otal-otal, harkar sufuri, kananan kasuwanni da suka rufe.

"Tattalin arziki ya gurgunce. Hakan zai kara haifar da mummunan yanayin tsaro.”

John Okon, wani mai sharhi ya ce mai yiwuwa an yi asarar sama da Naira miliyan 50 a cikin kwanaki biyu ya zuwa yanzu musamman ganin yadda wutar lantarki ta dakata kuma gidajen mai ke rufe.

Duba da tafka asarar da aka yi, gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Mallam Nasir Ahmad El-Rufai ta yi Allah wadai da zanga-zangar ta kungiyar kwadago, tare da kokawa kan irin barnar kungiyar ta yi jihar, kamar yadda gwamnan ya wallafa a shafin Twitter.

KU KARANTA: NITDA Ta Gargadi 'Yan Najeriya Game da Sabbin Ka'idojin Sirri Na WhatsApp

A wani labarin, Kungiyar Dattawan Arewacin Nigeria, ACF, a jiya Litinin, ta goyi bayan matakin da gwamnonin kudu suka ɗauka na hana kiwo a fili a jihohinsu 17, Daily Trust ta ruwaito.

ACF ɗin, cikin sanarwar da shugaban ta Cif Audu Ogbeh ya fitar ta ce ta amince da matakin domin an yi hakan ne don kiyaye kayan amfanin manoma.

Ogbeh ya ce, "Maganan gaskiya shine rikicin ya samo asali ne saboda mafi yawancin makiyaya sunyi imanin cewa sun da damar shiga kowanne gona su yi kiwo, su yi fyaɗe ko kashe duk wani da ya nemi hana su. Babu wanda zai amince da hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel