Yajin aikin Kaduna: Ka sasanta da kungiyar kwadago, gwamnonin APC sun shawarci El-Rufai

Yajin aikin Kaduna: Ka sasanta da kungiyar kwadago, gwamnonin APC sun shawarci El-Rufai

- Gwamnonin APC sun shawarci takwaransu na jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da ya hau teburin sulhu da kungiyar kwadago

- An samu sabani dai tsakanin gwamnan na Kaduna da kungiyar NLC sakamakon sallamar ma’aikata 4,000 a fadin kananan hukumomin 23 na jihar

- Lamarin ya tursasa kungiyar shiga yajin aiki inda ta tsayar da harkoki cak a jihar

- Kungiyar gwamnonin APC ta yi kira ga bangarorin biyu da su janye makamansu duba ga irin koma bayan da hakan zai kawo ta bangaren kudaden shiga

Kungiyar gwamnonin APC (PGF) ta shawarci Nasir el-Rufai, gwamnan Kaduna, da ya tattauna da kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) don magance yajin aiki a jihar.

Gwamna da ma’aikata sun samu sabani kan matakin da gwamnatin Kaduna ta dauka na sallamar ma’aikata 4,000 a fadin kananan hukumomin 23 na jihar.

Gwamnatin jihar ta bayyana batun karin albashi da sauransu a matsayin dalilin sallamar aikin - ci gaban da bai yi wa kungiyar kwadagon dadi ba.

Yajin aikin Kaduna: Ka sasanta da kungiyar kwadago, gwamnonin APC sun shawarci El-Rufai
Yajin aikin Kaduna: Ka sasanta da kungiyar kwadago, gwamnonin APC sun shawarci El-Rufai Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: INEC ta koka, ta ce babban zaben 2023 na iya samun matsala

Sakamakon haka, kungiyar kwadago ta NLC ta yanke shawarar tsayar da harkoki a jihar tare da yajin aikin gargadi na kwanaki biyar wanda suka fara a ranar Lahadi. An kuma gabatar da zanga-zangar nuna adawa da hukuncin a ranar Litinin a Kaduna.

Zanga-zangar ta sake daukar wani salo a ranar Talata lokacin da el-Rufai ya ayyana Ayuba Wabba, shugaban NLC, da sauran mambobin kungiyar a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo.

Da yake magana kan ci gaban, Kungiyar ta lura cewa yanzu ba lokacin “musayar karfi bane”, la’akari da raguwar kudaden shiga na jihohi, jaridar The Cable ta ruwaito.

Abubakar Bagudu, gwamnan jihar Kebbi kuma shugaban kungiyar, ya yi kira ga shugabannin kungiyar ta NLC da su fahimci kalubalen da kasar ke fuskanta.

Gwamna Bagudu ya yi wannan kiran ne a ranar Talata, 18 ga watan Mayu, a Abuja, jaridar Premium Times ta ruwaito.

"PGF na bin diddigin ci gaban da ke tsakanin NLC da gwamnatin jihar Kaduna a kan batun rage ma'aikatan kananan hukumomi da ke da matukar damuwa," in ji shi a cikin sanarwar.

“Lura da dukkan kalubalen da ke fuskantar dukkan jihohinmu, musamman ma da yake ana samun raguwar kudaden shiga, muna kira ga duk’ yan Najeriya masu kishin kasa, gami da kungiyar kwadago ta NLC, da su nuna jajircewa wajen tataunawa da gwamnatoci a dukkan matakai don magance matsalolin.

"Wannan ba lokaci ba ne na gwada karfi," in ji Bagudu, yana mai cewa tuni 'yan Najeriya suka shiga wani hali da tarin matsaloli.

“A wannan mawuyacin lokaci na tafiyarmu ta dimokiradiyya, ba za a iyakance tataunawa tsakanin dukkan gwamnatoci da‘ yan kasa ba.

“Muna kira ga shugabannin NLC da su gane cewa nauyin jagoranci shine magance kalubale bisa la’akari da halin gaskiya na gyara kurakuran da suka gabata.

“A matsayinmu na gwamnoni masu son ci gaba, muna da irin hangen nesan da gwamnatin jihar Kaduna ke yi na yin garambawul ga dukkanin majalisun kananan hukumominmu don ganin sun inganta su ta yadda za su iya samar da ci gaba.

KU KARANTA KUMA: Wata kungiyar jama’a ta caccaki MURIC, ta ce Musulmi ba zai gaji Buhari ba

"A lokaci guda, muna son yin kira ga gwamnatin jihar karkashin jagorancin abokin aikinmu, Malam Nasir El-Rufai da ta dauki duk matakan da suka dace don tabbatar da warware duk wata rashin jituwa don ra’ayin 'yan kasa a Kaduna."

A gefe guda, mun ji cewa wasu ‘Yan daba da aka yo haya sun tarwatsa zanga-zangar lumana da kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) ta fara a jihar Kaduna, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A yayin da zanga-zangar ke gudana, sai wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka shigo wajen a motoci biyu da adaidaita sahu inda suka fara jifan masu zanga-zangar.

Wasu daga cikin maharan sun rufe fuskokinsu dauke da wukake da sanduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng