NITDA Ta Gargadi 'Yan Najeriya Game da Sabbin Ka'idojin Sirri Na WhatsApp

NITDA Ta Gargadi 'Yan Najeriya Game da Sabbin Ka'idojin Sirri Na WhatsApp

- Hukumar NITDA ta shawarci 'yan Najeriya game da ba da bayanan sirri a kafafen sada zumunta

- Hukumar ta kuma gargagadi 'yan Najeriya kan amfani da WhatsApp wajen yada bayanansu na sirri

- Ta kuma bayyana cewa, 'yan Najeriya na da zabin amfani da wasu shafukan sada zumunta sabanin WhatsApp

Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA) ta shawarci ’yan Najeriya kan yadda za su kauce wa fadawa cikin matsalar mulkin mallaka na zamani, jaridar Punch ta ruwaito.

Hukumar NITDA ta shawarci masu amfani da shafukan sada zumunta, musamman WhatsApp da su guji musayar bayanansu na sirri a wadannan shafuka.

Hukumar ya yi gargadin cewa cewa wa'adin farko (na wadannan dandamali) na sirri da tsaro yanzu haka an mamaye su bisa tushen fifita kasuwanci.

Ta yi wannan gargadin ne a cikin wata sanarwa da shugabar Harkokin kamfanoni da alakar waje, Hadiza Umar ta fitar.

KU KARANTA: Hukumar Hisbah Ta Kame Mata da Miji Masu Safarar Jarirai a Jihar Kano

NITDA Ta Gargadi 'Yan Najeriya Game da Sabbin Ka'idojin Sirri Na WhatsApp
NITDA Ta Gargadi 'Yan Najeriya Game da Sabbin Ka'idojin Sirri Na WhatsApp Hoto: today.ng
Asali: UGC

NITDA ta ce tana jin nauyi ne a kanta ta samar da shawarwari ga 'yan Najeriya kan sauye-sauyen ka'idojin aiki da tsarin sirri na WhatsApp wanda ya fara aiki daga 15 ga Mayu, 2021.

Miliyoyin 'yan Najeriya suna amfani da dandalin WhatsApp don kasuwanci, zamantakewa, ilimantarwa da wasu dalilai.

NITDA ta ce, tare da hadin gwiwar Kungiyar Hadin Gwiwar Afirka ta Kula da Bayanai, sun gana da Facebook, masu WhatsApp, a ranar 9 ga Afrilu, 2021 kuma a matsayinta na mai kula da bayanan sirrin Najeriya, ta ji bukatar ba 'yan Najeriya shawara kan lamarin.

NITDA ta fadawa ‘yan Najeriya cewa suna da 'yanci su yanke shawara kan bada izinin sarrafa bayanansu.

Sanarwar ta kara da cewa, “Masu amfani da Whatsapp na da 'yanci su yanke shawara kan bayar da izinin sarrafa bayanansu dangane da sabuwar manufar tsare sirri.

"Masu amfani da shafukan za su kasance a karkashin sharudda da manufofin Facebook da sauran kungiyoyin karbar bayanai tare da ko ba tare da kasancewa wadanda suka nemi ayyukan kai tsaye ba."

NITDA ta sake nanata cewa 'yan Najeriya suna da zabin amfani da wasu shafukan sanda zumuntan sabanin WhatsApp.

Hukumar ta kuma shawarci 'yan Najeriya da su takaita raba bayanan sirri a kan sakonni a dandalin sada zumunta, musamman tunda an fifita kasuwanci a kan sirri da tsaro.

KU KARANTA: Gwamnonin PDP: Muna Son Buhari Ya Amince da Yiwa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima

A wani labarin, A shekarar da ta gabata lokacin da Bill Gates ya bar shugabancin kamfanin Microsoft, ya ce aikin agaji ne ya sa ya yanke shawarar, amma sabon rahoto na danganta ficewar tashi da wani lamari da ya faru kusan shekaru 20 da suka gabata.

An ce yana karkashin bincike game da lamarin a shekarar 2019, yayin da kwamitin Microsoft ya nemi Gates ya sauka daga shugabancin kamfanin yayin da binciken ke gudana.

Maganar da ake zarginsa dashi ta kasance tare da wata injiniyar kamfanin Microsoft da ba a bayyana sunanta ba, wacce ta bayyana alakarta da shi a wata wasika. Lamarin ya bayyana ne yayin da Gates da matarsa, Melinda, ke fuskantar cuku-cukun saki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel