Rikici Ya Barke Tsakanin 'Yan Bindiga Sun Yi Musayar Wuta, Sun Hallaka Junansu a Neja

Rikici Ya Barke Tsakanin 'Yan Bindiga Sun Yi Musayar Wuta, Sun Hallaka Junansu a Neja

- 'Yan bindiga dake addabar mutanen jihar Neja sun yi musayar wuta tsakaninsu sun kashe kansu

- Rahoto ya bayyana cewa, rikici ne ya barke tsakaninsu, inda wasu suka yi yunkurin kashe shugabansu

- Akalla mutane 12 suke mutu a rikicin yayin da wasu da dama suka ji raunuka kuma suka tsere daga dajin

'Yan bindiga da ke addabar al'ummomin jihar Neja a karshen mako sun bude wa juna wuta, inda suka kashe mutane 12 a karamar hukumar Shiroro. Baya ga wadanda aka kashe, wasu da yawa sun sami raunuka daban-daban amma sun tsere daga "filin yakin".

Wannan lamarin da ya faru a ranar Juma'ar da ta gabata, ya haifar da bacewar wasu 'yan bindiga daga a yankin.

Jaridar Vanguard ta ruwaito daga wata majiya a kauyen cewa an samu rashin jituwa sosai tsakanin shugaban 'yan bindigan da yaransa kan kudin fansar da aka biya su.

Shugaban, wanda aka fi sani da Mallam Dogogide, ya zargi yaransa da canza masa wuri bayan ayyukan da suka yi a baya.

KU KARANTA: Gwamnonin PDP: Muna Son Buhari Ya Amince da Yiwa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima

Rikici Ya Barke Tsakanin 'Yan Bindiga Sun Yi Musayar Wuta, Sun Hallaka Junansu a Neja
Rikici Ya Barke Tsakanin 'Yan Bindiga Sun Yi Musayar Wuta, Sun Hallaka Junansu a Neja Hoto: signalng.com
Asali: UGC

An ce Dogogide yana daya daga cikin shugabannin wasu gungun 'yan bindiga uku da ke aiki a tsakanin kananan hukumomin Shiroro, Rafi da Munya a jihar Neja da Birnin Gwari a jihar Kaduna.

An kuma tattaro cewa Dogogide ya nuna fushinsa ga dokokin da aka shimfida ta hanyar kashe mazauna kauyukan tare da yiwa matan aure fyade.

Jin haushin wannan, ya kira samarinsa don ganawa kuma yayi barazanar sallamarsu tare da maye gurbinsu da sabbin ma'aikata. Hakan, bai yi wa yaransa dadi ba kuma an ce wannan ne ya haifar da zazzafan cece-kuce.

An tattaro cewa ana cikin hakan ne, daya daga cikin yaran sa yayi yunkurin kashe shi lokacin da ya bude wuta amma maigidan nasa ya kaucewa harsashin.

Masoyan shugaban wadanda suka fusata da rashin biyayya ga Dogogide sun yi ta fafutukar kare shugaban nasu, inda suka bude wuta suka harbe 12 daga cikin wadanda suka fusata, yayin da wasu suka tsere.

Majiyar ta ci gaba da bayyana cewa wasu daga cikin ‘yan bindigan daga baya sun afkawa wani kauye bayan “yakin” inda suka yi awon gaba da mutum goma don taimakawa wajen binne gawarwakin 'yan uwansu.

An saki mutanen goma da aka sace bayan an binne gawarwakin yayin da 'yan bindigan suka gudu daga cikin garin.

An ce wasu daga cikin mazauna kauyen sun tsere daga yankin saboda tsoron kada 'yan ta'addan daga baya su mamaye yankinsu su kashe su.

KU KARANTA: NITDA Ta Gargadi 'Yan Najeriya Game da Sabbin Ka'idojin Sirri Na WhatsApp

A wani labarin, Hukumar Hisbah ta cafke wata mata da mijinta da suka yiwo safarar wata jariyiya daga Jihar Delta zuwa Kano, Aminiya ta ruwaito.

Jami’an Hukumar ta Jihar Kano sun cafke mata da mijin ne a tashar mota bayan da suka lura da alamar tambaya tattare da ma’auratan.

Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Harun Ibn-sina, ya ce, “Kafin su amsa laifin safarar jaririyar, da farko ma’auratan sun yi ikirarin cewa su suka haife ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.