Hukumar Hisbah Ta Kame Mata da Miji Masu Safarar Jarirai a Jihar Kano

Hukumar Hisbah Ta Kame Mata da Miji Masu Safarar Jarirai a Jihar Kano

- Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kame wata mata da mijinta dake safarar jarirai zuwa Kano

- An kame su ne dauke da wata jaririya da suka yi safararta daga jihar Delta zuwa jihar Kano

- Tuni Hisbah ta tura su ga hukumar 'yan sanda don a ci gaba da gudanar cikakken bincike

Hukumar Hisbah ta cafke wata mata da mijinta da suka yiwo safarar wata jariyiya daga Jihar Delta zuwa Kano, Aminiya ta ruwaito.

Jami’an Hukumar ta Jihar Kano sun cafke mata da mijin ne a tashar mota bayan da suka lura da alamar tambaya tattare da ma’auratan.

Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Harun Ibn-sina, ya ce, “Kafin su amsa laifin safarar jaririyar, da farko ma’auratan sun yi ikirarin cewa su suka haife ta.

KU KARANTA: Gwamnoni 13 Na PDP Sun Shiga Taron Sirri Don Tattauna Matsalar Rashin Tsaro

Hukumar Hisbah Ta Kame Mata da Miji Masu Safarar Jarirai a Jihar Kano
Hukumar Hisbah Ta Kame Mata da Miji Masu Safarar Jarirai a Jihar Kano Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

"Bayan da aka titsiye su, sai suka amsa cewar sayen jaririyar suka yi N900,000 a wajen wata malamar asibiti a Jihar Delta.”

Ibn-Sani wanda ya ce an kama ma’auratan ne a ranar Litinin, ya ce Hukumar ta mika su ga Hedikwatar ’Yan Sandan Jihar Kano don ci gaba da bincike.

Ya bukaci jama’ar jihar da su rika taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri game duk wani abu da ba su yarda da shi ba.

Ibn-Sina, ya kuma shawarci iyaye da su rika sanya ido sosai kan ’ya’yansu don gudun fadawa hannun masu satar yara.

KU KARANTA: Da Duminsa: 'Yan Sanda Sun Ceto Farfesan UNIJOS da Mijinta Daga 'Yan Bindiga

A wani labarin, A shekarar da ta gabata lokacin da Bill Gates ya bar shugabancin kamfanin Microsoft, ya ce aikin agaji ne ya sa ya yanke shawarar, amma sabon rahoto na danganta ficewar tashi da wani lamari da ya faru kusan shekaru 20 da suka gabata.

An ce yana karkashin bincike game da lamarin a shekarar 2019, yayin da kwamitin Microsoft ya nemi Gates ya sauka daga shugabancin kamfanin yayin da binciken ke gudana.

Maganar da ake zarginsa dashi ta kasance tare da wata injiniyar kamfanin Microsoft da ba a bayyana sunanta ba, wacce ta bayyana alakarta da shi a wata wasika. Lamarin ya bayyana ne yayin da Gates da matarsa, Melinda, ke fuskantar cuku-cukun saki.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel