Ba zan taba barin Gwamna El-Rufai ya shigo gidana ba, Sheikh Dahiru Bauchi

Ba zan taba barin Gwamna El-Rufai ya shigo gidana ba, Sheikh Dahiru Bauchi

- Fitaccen Malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi ya ce ba zai taba barin El-Rufai shiga gidansa ba

- Ya sanar da hakan ne yayin da ya karba bakunci tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido a gidansa dake Bauchi

- Malamin ya zargi El-Rufai da kwashe masa almajirai tare da muzgunawa mazauna gidansa saboda makaranta Qur'ani ne

Fitaccen Malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, yace babu dalilin da zai sa ya bar Gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai ya shiga gidansa idan da ya biyo tawagar tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi.

Idan za mu tuna jami'an jihar Kaduna dake tabbatar da yaki da bara sun shiga makarantar malamin inda suka kwashe almajirai a shekarar da ta gabata, Vanguard ta wallafa.

Sheikh Bauchi ya sanar da hakan ne a gidansa dake Bauchi a ranar Litinin yayin da ya karba bakuncin tsohon sarkin wanda aka nada Khalifan Tijjaniya a Najeriya.

"Ina El-Rufai? A zatona ai zai biyo tawagarka, da na sa masu gadi sun hana shi shigowa koda farfajiyar gidan nan. Ya kori dalibai masu koyon karatun Qur'ani, ya zuba su a daji kuma ya dawo gidana ya hantari mutanen dake ciki saboda kawai makaranta Qur'ani ne," Sheikh Dahiru yace.

Ba zan taba barin Gwamna El-Rufai ya shigo gidana ba, Sheikh Dahiru Bauchi
Ba zan taba barin Gwamna El-Rufai ya shigo gidana ba, Sheikh Dahiru Bauchi. Hoto daga @TheCableng
Asali: UGC

KU KARANTA: Jonathan: Ban taba amfani da matsayina wurin musgunawa wani ba ko azabtarwa ba

A bangarensa, Alhaji Lamido Sanusi ya roki yafiya a madadin abokinsa inda yace yana da tabbacin gwamnan bai san abinda ya faru ba, kamra yadda jaridar ThisdayLive ta ruwaito.

"El-Rufai baya kasar lokacin da lamarin ya faru, nima bana Najeriya yayin da hakan ta faru. Ina tabbatar maka da cewa hakan ba zai sake faruwa ba. Ina rokon yafiya a madadin abokina kuma aminina.

"Ina fatan lamarin bai shiga har zuciyarka ba saboda abun ba zai yi dadi ba idan hakan ta faru. Babu wanda zai yi fatan ya zama makiyi a idanun mutum irinka. Ka yafe mishi har cikin zuciya," Sabon shugaban Tijjaniyan ya roka.

Mun yi yunkurin tuntuban Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin jin ta bakinsa kan wannan amari amma abin ya ci tura.

KU KARANTA: Allah yayi wa zukekiyar jarumar Kannywood, Khadija Mahmud, rasuwa

A wani labari na daban, kafin fara yajin aikin kwanaki biyar na jan kunne da kungiyar kwadago ta Najeriya ta shirya farawa a ranar Litinin a jihar Kaduna, Gwamna Nasir El-Rufai yace ya shirya kuma yana jiran shugabannin kungiyar kwadagon da na jam'iyyar adawa ta PDP.

Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar rarrabe wutar lantarki ta Najeriya ta fada yajin aikin tun tsakar daren Asabar kuma ta tsinke dukkan layikanta da suke hade da jihar, lamarin da ya bar jama'ar jihar cikin duhu.

Wannan ya biyo bayan jan kunnen da kungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta kasa ta yi kuma ta bayyana cewa zata bi ayarin NLC wurin tafiya yajin aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng