Yajin aikin ma'aikatan Kaduna: Mun shirya muku, El-Rufai ga NLC, PDP

Yajin aikin ma'aikatan Kaduna: Mun shirya muku, El-Rufai ga NLC, PDP

- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya sanarwa PDP da kungiyar kwadago a shirye yake

- Kamar yadda ya fadi, gwamnatinsa ba za ta tankwaru da bacin suna ko kuma wasu karairayi ba da ake shirya musu

- Gwamnan yace babu hankali a ce ya zuge kashe 84 ko 96 na abinda jihar ke samu daga gwamnatin tarayya domin biyan albashi

Kafin fara yajin aikin kwanaki biyar na jan kunne da kungiyar kwadago ta Najeriya ta shirya farawa a ranar Litinin a jihar Kaduna, Gwamna Nasir El-Rufai yace ya shirya kuma yana jiran shugabannin kungiyar kwadagon da na jam'iyyar adawa ta PDP.

Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar rarrabe wutar lantarki ta Najeriya ta fada yajin aikin tun tsakar daren Asabar kuma ta tsinke dukkan layikanta da suke hade da jihar, lamarin da ya bar jama'ar jihar cikin duhu.

Wannan ya biyo bayan jan kunnen da kungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta kasa ta yi kuma ta bayyana cewa zata bi ayarin NLC wurin tafiya yajin aikin.

KU KARANTA: Na Allah basu karewa: Dan sanda ya mayar da N1.2m da ya tsinta wurin hatsari a Kano

Yajin aikin ma'aikatan Kaduna: Mun shirya muku, El-Rufai ga NLC, PDP
Yajin aikin ma'aikatan Kaduna: Mun shirya muku, El-Rufai ga NLC, PDP. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

A ranar Asabar El-Rufai yace gwamnatinsa ba za ta saurari kowanne irin bacin suna ba, tare da jaddada cewa ba zai yuwu ya kashe kashi 84 zuwa 96 na kudin da yake samu daga gwamnatin tarayya ba zuwa biyan albashi.

Gwamnatin jihar tace ana ta gangamin shirya mata karairayi da ikirari marasa tushe inda aka ce ta sallama ma'aikata 4000 kuma ta daina biyan sabon mafi karancin albashi.

Daily Trust ta ruwaito cewa a kalla ma'aikatu 14 ne da suka hada da na jiragen sama, man fetur, bankuna, asibitoci da fannin sufuri suka bayyana cewa sun shirya shiga yajin aikin.

Shugaban kungiyar kwadago, Ayuba Wabba da sauran shugabannin sun dira jihar Kaduna a ranar Lahadi domin shiga ganawar sirri da ma'aikata.

Amma a wata wallafar da PDP tayi a Twitter, ta ce 'za a shiga gagarumin yajin aiki' a jihar Kaduna. Sai dai el-Rufai ya kwatanta NLC da PDP da 'gagaruman munafukai' inda ya jaddada cewa jihar Kaduna tana jiransu.

KU KARANTA: Bauchi: Sarki ya dakatar da Wakilin Birni saboda zarta shi walkiya yayin hawan sallah

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun kai farmaki fadar Kindred na Jor Fada, Terhile Atser dake Gboko. Sun lalata kadarorin miliyoyin naira yayin da suka kai harin a cikin ranakun karshen mako.

Fadar shugaba Kindred tana nan a lamba 36 titin Kyado, Gboko ta gabas, karamar hukumar Gboko ta jihar Binuwai.

Kadarorin da suka salwanta yayin harin sun hada da motoci, babura da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel