Jonathan: Ban taba amfani da matsayina wurin musgunawa wani ba ko azabtarwa ba
- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yace bai taba amfani da matsayinsa ba wurin azabtarwa ko ladabtar da kowa ba
- Tsohon shugaban kasan Najeriyan yace mulki dan wucin-gadi ne kuma Ubangiji ne kadai ke baiwa mutum
- Jonathan yace har yanzu ana jinjina masa ta yadda bai taba musgunawa ko azabtar da kowa ba yayin mulkinsa
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan yace a yayin da yake mulki ya sha alwashin ba zai taba amfani da matsayinsa ba wurin ladabtar da jama'a ba ko musguna musu.
Jonathan wanda ya shugabanci Najeriya daga 2010 zuwa 2015 ya kwatanta mulkin da ya samu a matsayin wata dama ta wucin-gadi da Ubangiji ya bashi, TheCable ta ruwaito.
Ya sanar da hakan ne yayin jawabi a bikin murnar cika shekaru 50 na Charles Osazuwa, shugaban cocin Rock of Ages Christian Assembly da aka yi a Benin, jihar Edo a ranar Lahadi.
KU KARANTA: Rashin tsaro: Lalong ya bayyana abinda marigayi Dogonyaro ya sanar da shi
Tsohon shugaban kasan yace har a halin yanzu ana magana akan halayyarsa na kin amfani da matsayinsa wurin kashe wani.
"Abinda na yarda dashi bayan na shiga siyasa shine, bazan yi amfani da matsayina na wucin-gadi da Ubangiji ya bani ba wurin ladabtar da jama'a ba," yace.
"Duk wani mukami da na samu daga hukuncin Ubangiji, bana amfani dashi wurin musgunawa jama'a ko tsawwala musu."
A jawabinsa, Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo, ya jinjinawa Osazuwa da yadda yayi amfani da fadin Ubangiji wurin yin magana a kan kalubalen da kasar nan ke fuskanta.
"Abinda yasa Osazuwa ka fita daban shine yadda kake alakanta kalubalen kasar nan da fadin Ubangiji kuma kake nuna mana komai mai wucewa ne," yace.
"Osazuwa ya fahimci yadda Ubangiji yake da kuma kalmominsa ke tasiri a wannan zamanin. Babu wanda ya taba amfani da irin wannan salon wurin bayanin nan."
Ifeanyi Okowa, Gwamnan jihar Delta, ya jinjinawa Osazuwa a kan yadda yake amfani da cocinsa wurin gyara rayuwar jama'a.
Osazuwa yayi kira ga 'yan siyasa da su sassautawa jama'a ko talaka ya samu saukin rayuwa.
KU KARANTA: Kurunkus: 'Yan bindiga sun bayyana masu basu makamai kuma suke raba kudin fansa
A wani labari na daban, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya ce "dukkan 'yan Najeriya" ne suke bukatarsa da ya nemi kujerar shugabancin kasa a zaben 2023 mai zuwa.
A yayin jawabi a ranar Juma'a yayin da ake yin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels, Bello ya ce zai bada ansa ga wannan bukatar nan babu dadewa.
Gwamnan yace 'yan Najeriya suna bukatar dan takara da zai hada kan kasar nan, kuma ya yadda yana da dukkan nagartar da ake bukata domin zama shugaban kasa.
Asali: Legit.ng