Wakilin Birnin Bauchi: Gwamnan Bauchi Ne Ya Kitsa Yadda Aka Dakatar Dani

Wakilin Birnin Bauchi: Gwamnan Bauchi Ne Ya Kitsa Yadda Aka Dakatar Dani

- Biyo bayan dakatar dashi, wakilin Birnin Bauchi ya bayyana cewa, akwai siyasa cikin batun

- Ya ce tabbas akwai hannun gwamnan jihar Bauchi a dakatarwar da aka yi masa a bayan Sallah

- Sai dai, gwamnatin Bauchi ta musanta zargin, tana mai cewa batu ne da bai da tushe ko kadan

Majalisar masarautar Bauchi ta dakatar da mamba mai wakiltar mazabar Bauchi ta Tarayya a majalisar wakilai, Yakubu Shehu Abdullahi, a matsayin mai rike da sarautar Wakilin Birnin Bauchi har sai baba ta gani.

A wani martani da ya yi, Abdullahi ya yi zargin cewa Gwamna Bala Mohammed na da hannu a dakatarwar saboda ya ki shiga jam'iyyar PDP bayan ya bar Jam’iyyar PRP inda a maimakon haka ya koma tsohuwar Jam’iyyarsa ta APC.

"Lokacin da na fice daga PRP gwamnan ya nemi na hade da shi a PDP amma na fada cewa zan koma APC saboda jam'iyata ce kuma mutanen da suka yi rashin adalci a kanmu ba su nan," in ji shi.

KU KARANTA: Matafiya Sun Shiga Mawuyacin Hali Sakamakon Yajin Aikin Kwadago a Jihar Kaduna

Korarren Wakilin Birnin Bauchi: Da Sa Hannun Gwamna Aka Kitsa Dakatar Dani
Korarren Wakilin Birnin Bauchi: Da Sa Hannun Gwamna Aka Kitsa Dakatar Dani Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Dangane da zargin na Abdullahi, mai ba Mohammed shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya kira zargin mara tushe.

Ya ce dalilin dakatar da Abdullahi shi ne kamar yadda ya bayyana a wasikar dakatarwa daga masarautar - rashin girmamawa ga sarki, majalisar masarauta da kuma masarautar gargajiya.

“Me ya sa bai bayyana batun gwamnan da ya nemi ya koma PDP ba har zuwa yanzu?

"Yana da damar shiga kowace jam’iyya kuma babu wanda zai ci zarafinsa saboda zabin jam’iyyarsa, gwamnan ba shi da wata alaka da dakatarwar da aka yi masa kuma ya kamata ya je ya fuskanci majalisar masarautar,” in ji Gidado.

Dakatarwar na kunshe a cikin wasika mai sakin layi uku tare da lamba BEC/ADM/20/VOL.X

Abdullahi ya shaida wa Daily Trust cewa dakatarwar na da nasaba da siyasa saboda “an hana ni da sauran mukarrabai na shiga gidan Gwamnati a lokacin da ake yi wa gwamnan gaisuwar Sallah a ranar Asabar.”

Tuni dai Abdullahi ya yi ikirarin a ba shi damar yin bayani kafin majalisar ta yanke hukunci.

"Kwamitin ya dauki matakin ne ba tare da jin bangare na ba don adalci saboda jami'an tsaro sun hana ni da mukarrabai na mu kadai shiga gidan Gwamnati, lamarin da ya tilasta min saukowa daga kan doki na da kuma takawa zuwa wurin taron."

Abdullahi ya kara da cewa duk da tsoma bakin da wasu jami’an gwamnati suka yi a bakin kofar, “jami’an tsaron sun dage cewa akwai umarni daga sama cewa kada su bari ni da tawaga ta mu shiga gidan gwamnati.

A cewarsa bai yi mamaki ba saboda "Gwamna Bala Mohammed ya gaya mini cewa shi da kansa zai nuna rashin amincewa da sarautata ta gargajiya ta Wakilin Birni a gaban Sarkin Bauchi wanda ya yi daidai da lakabin babban yayansa na Wakilin Bauchi; Alhaji Adamu Muhammad."

KU KARANTA: 'Yan Ta'addan IPOB Sun Kashe 'Yan Sanda 2, Sun Kona Ofishin 'Yan Sanda

A wani labarin daban, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) a jiya ta yi zargin cewa gwamnatin jihar Kaduna na shirin kutsa kai cikin zanga-zangarta tare da tura ‘yan daba, The Nation ta ruwaito.

Sanarwar ta ce an yaudaru ne wajen yaba wa gwamnatin Nasir El-Rufai saboda kasancewa ta farko da ta fara biyan sabon mafi karancin albashin N30,000.

NLC, a cikin wata sanarwa ta bakin Shugabanta na Majalisar Jihar Kaduna, Ayuba Suleiman, ya ce tun tunu jihar ta sake komawa ga tsohon tsarin albashin N18, 000 ga wasu ma’aikatan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel