Gwamnoni 13 Na PDP Sun Shiga Taron Sirri Don Tattauna Matsalar Rashin Tsaro
- Wasu gwamnoni a karkashin inuwar jam'iyyar PDP sun shiga tattaunawar sirri kan batun tsaro
- Gwamnonin 13 suna ganawa ne a jihar Oyo, inda ake sa ran isowar wasu sauran gwamnonin
- Ana sa ran za su tattauna kan batun rashin tsaron Najeriya da kuma ci gaban jam'iyyarsu ta PDP
Gwamnonin jihohi 13 a karkashin jam'iyyar PDP, a yanzu haka suna ganawa a Cibiyar Taron Kasa da Kasa na Cibiyar Kula da Noma ta IITA dake Ibadan ranar Litinin, Daily Nigerian ta ruwaito.
Gwamnonin su ne: Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato; Samuel Ortom na Benue; Douye Diri na Bayelsa; Okezie Ikpeazu na Abia da Emmanuel Udom na Akwa Ibom.
Sauran sune: Ifeanyi Okowa na Delta, Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, Umar Fintiri na Adamawa; Bala Mohammed na jihar Bauchi, Nyesom Wike na Ribas da Godwin Obaseki na Edo.
Akwai kuma gwamna mai masaukin baki, Seyi Makinde na Jihar Oyo da Mataimakin Gwamnan Zamfara, Aliyu Gusau wanda ya wakilci Gwamna Bello Matawalle.
KU KARANTA: 'Yan Ta'addan IPOB Sun Kashe 'Yan Sanda 2, Sun Kona Ofishin 'Yan Sanda
Ana sa ran Gwamna Darius Ishaku, na Taraba da Gwamna Ben Ayade, na Kuros Riba za su shigo yayin da taron ke ci gaba.
Gwamnonin da suka iso cibiyar taron daidai karfe 1:10 na rana a cikin motar bas sun shiga ganawar sirri.
NAN ta tattaro daga wurin taron cewa taron zai mayar da hankali ne kan yanayin tsaro a kasar.
Ta kuma tattaro cewa taron wanda Shugaban gamayyar gwamnonin PDP ya jagoranta, Gwamna Aminu Tambuwal zai tattauna wasu batutuwan da suka shafi ci gaban jam'iyyar.
Ana sa ran za a fitar da sanarwa bayan taro.
KU KARANTA: Matafiya Sun Shiga Mawuyacin Hali Sakamakon Yajin Aikin Kwadago a Jihar Kaduna
A wani labarin, Majalisar masarautar Bauchi ta dakatar da mamba mai wakiltar mazabar Bauchi ta Tarayya a majalisar wakilai, Yakubu Shehu Abdullahi, a matsayin mai rike da sarautar Wakilin Birnin Bauchi har sai baba ta gani.
A wani martani da ya yi, Abdullahi ya yi zargin cewa Gwamna Bala Mohammed na da hannu a dakatarwar saboda ya ki shiga jam'iyyar PDP bayan ya bar Jam’iyyar PRP inda a maimakon haka ya koma tsohuwar Jam’iyyarsa ta APC.
"Lokacin da na fice daga PRP gwamnan ya nemi na hade da shi a PDP amma na fada cewa zan koma APC saboda jam'iyata ce kuma mutanen da suka yi rashin adalci a kanmu ba su nan," in ji shi.
Asali: Legit.ng