Da Ɗuminsa: Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Wani Tsohon Soja Dake Horad da Yan Ta'addan IPOB

Da Ɗuminsa: Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Wani Tsohon Soja Dake Horad da Yan Ta'addan IPOB

- Rundunar yan sanda ta samu nasarar cafke wani tsohon jami'in soja da aka kora da zargin bayar da horo ga jami'an IPOB

- Tsohon sojan ya amsa laifinsa inda yace mambobin IPOB ne suka ɗaukeshi aiki da alƙawarin biyansa albashin daya ninka wanda yake amsa lokacin yana soja

- Ya kuma bayyana cewa ya horad da jami'an tsaron ESN aƙalla 2,000 daga lokacin da ya fara aikin

Rundunar yan sanda ta cafke wani korarren soja da take zargin yana da hannu wajen horad da jami'an tsaron ESN, na ƙungiyar kafa ƙasar Biafara IPOB.

KARANTA ANAN: Yajin Aiki: An Kulle Sakatariyar Gwamnatin Kaduna, Mambobin NLC Sun Mamaye Kan Hanyoyi

Rahoton Premium Times ya gano cewa an kama mutumin kwanaki kaɗan kafin a kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin yan ta'addan, Awurum Eze, wanda aka kama a Aba, jihar Abia.

Tawagar jami'an ESN ɗin ne ake zargi da kai munanan hare-hare kan jami'an yan sanda tare da kashe su da kuma lalata kayan aikinsu a yankin kudu-kudu da kudu-gabas.

Da Ɗuminsa: Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Wani Tsohon Soja Dake Horad da Yan Ta'addan IPOB
Da Ɗuminsa: Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Wani Tsohon Soja Dake Horad da Yan Ta'addan IPOB Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wata majiya ta bayyana cewa, tsohon sojan ɗan kimanin shekara 32 wanda aka bayyana sunansa da, Livinus Owalum-Barnabas, ya shiga komar hukuma ne a Gwagwalada, Abuja ranar Lahadi.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Hukumar Zaɓe INEC, Sun Ƙona Motoci 6

Majiyar tace: "Mambobin IPOB ne suka ɗauki tsohon sojan aiki, sannan suka tura shi ya bada horo ga sabbin jami'ansu na IPOB/ESN dake sansanin bada horon su biyu a Abia da Delta."

Yayin da ya shiga hannu, tsohon sojan ya amsa laifinsa, yace IPOB ne suka ɗauke shi aiki tareda alƙawarin zasu biyashi ninkin abinda ake biyansa a rundunar soji.

Ya kuma bayyana cewa ya horad da jami'an ESN aƙalla 2,000 yadda zasu yi faɗa, amfani da makamai da kuma yaƙin sunƙuru.

A wani labarin kuma Ku Taimaka in Sauke Wannan Nauyin da Aka Ɗora Mun, Gwamna Masari

Gwamnan jihar Katsina , Aminu Bello Masari, ya roƙi al'ummar jihar sa su taimaka masa ya sauke nauyin shugabancin da suƙa ɗora masa.

Masari yace tun sanda ya shiga ofis ɗin gwamna a watan Mayu 2015, ya fara shirye-shiryen fita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel