Yajin Aiki: An Kulle Sakatariyar Gwamnatin Kaduna, Mambobin NLC Sun Mamaye Kan Hanyoyi

Yajin Aiki: An Kulle Sakatariyar Gwamnatin Kaduna, Mambobin NLC Sun Mamaye Kan Hanyoyi

- An kulle sakatariyar gwamnatin jihar Kaduna yayin da itama tashar jirgin ƙasa dake unguwar Rigasa take a kulle

- Mambobin ƙungiyar kwadugo sun cika titunan jihar Kaduna inda suke gudanar da zanga-zangar lumana kan matakin gwamnatin jihar na korar wasu ma'aikata

- Ƙungiyar ƙwadugo ta kasa ta ayyana shiga yajin aikin gargaɗi ne domin titastawa gwamnan jihar ya dawo da ma'aikatan

A yanzu haka mambobin ƙungiyar ƙwadugo ta ƙasa sun mamaye titunan jihar Kaduna inda suke cigaba da yajin aikin gargaɗi domin tilastawa gwamnati ta janye kudirinta na korar ma'aikatan.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Hukumar Zaɓe INEC, Sun Ƙona Motoci 6

An rufe tashar jirgin ƙasa dake unguwar Rigasa yayin da Sakatariyar gwamnatin jihar wadda ke ƙunshe da ma'aikatu goma take a rufe da kwaɗo.

Ma'aikata daga ɓangare daban-daban sun baiwa ƙungiyar kwadugo haɗin kai wajen tsunduma yajin aikin, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Yajin Aiki: An Kulle Sakatariyar Gwamnatin Kaduna, Mambobin NLC Sun Mamaye Kan Hanyoyi
Yajin Aiki: An Kulle Sakatariyar Gwamnatin Kaduna, Mambobin NLC Sun Mamaye Kan Hanyoyi Hoto: @bbchausa
Asali: Twitter

Kafin ma'aikatan su kwaranya kan titunan jihar, saida shugaban NLC na jihar Kaduna, Ayuba Sulaiman, ya gabatar da wani jawabi a garesu.

Hakanan shima shugaban ƙungiyar ƙwadugo ta ƙasa, Ayuba Waba, ya shiga cikin masu zanga-zangar a hedkwatar ƙungiyar ta jihar.

KARANTA ANAN: Ku Taimaka in Sauke Wannan Nauyin da Aka Ɗora Mun, Gwamna Masari

Ƙungiyar kwadugo ta tsunduma yajin aikin gargaɗi na kwana biyar ne bayan gwamnatin jihar Kaduna ta kasa canza ra'ayin ta a kan dawo da ma'aikatan da ta kora kwanakin baya.

Gwamnan jihar, Malam Nasiru El-Rufa'i ya bayyana cewa ba zai yuwu kuɗin da gwamnatin sa ke samu su ƙare a kan biyan albashi kaɗai ba.

A wani labarin kuma Babbar Magana: Zama Gwamna Ƙara Talautad Dani Yayi, Inji Tsohon Gwamna

Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, yace zaman shi gwamna na shekara takwas ƙara talautad dashi yayi.

Sanatan wanda yake wakiltar Imo ta yamma ya faɗi haka ne yayin da yake musanta zargin da ake masa cewa ya mallaki kadarori a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel