Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Hukumar Zaɓe INEC, Sun Ƙona Motoci 6

Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Hukumar Zaɓe INEC, Sun Ƙona Motoci 6

- Wasu yan bindiga sun kai hari hedkwatar hukumar zaɓe INEC ta jihar Enugu, inda suka ƙona Motocin Hilux shida dake harabar wajen

- Jami'an tsaro sun samu nasarar fatattakar maharan waɗanda suka yi ƙoƙarin kutsa kai cikin ginin ofishin

- Kwamishinan yan sandan jihar ya bada umarnin jibge yan sanda a yankin domin dawo da komai yadda yake

Kwana biyu bayan an lalata ofishin INEC a ƙaramar hukumar Udenu jihar Enugu, wasu yan bindiga sun sake kai hari hedkwatar hukumar ta jiha, inda suka ƙona motoci.

KARANTA ANAN: Kotu Ta Yankewa Musulmi 29 Hukuncin Kisa Saboda Rikici Kan Limancin Sallar Idi

Rahoton Punch ya gano cewa kimanin yan bindiga bakwai ne a cikin wata ƙaramar motar Bas suka farmaki hedkwatar INEC ɗin dake kusa da kafar watsa labarai ta jihar Enugu a Independence Layout.

Yan bindigan sun cinna wa motocin Hilux shida wuta, biyar daga cikinsu sun ƙone ƙurmus yayin da ɗaya bata gama ƙonewa ba.

Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Hukumar Zaɓe INEC, Sun Ƙona Motoci 6
Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Kai Hari Hedkwatar Hukumar Zaɓe INEC, Sun Ƙona Motoci 6 Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Rahoton ya bayyana cewa maharan sun yi ƙoƙarin ƙona ginin hedkwatar amma sai jami'an tsaron dake gadin wurin suka fatattake su.

Mazauna yankin sun ce sun jiyo ƙarar harbin bindiga da misalin ƙarfe 10:00 na dare kafin faruwar lamarin, amma basu gano su waye ke wannan harbin ba.

Kwamishinan INEC na jihar Enugu, Emeka Ononamadu, ya tabbatar da kai harin lokacin da aka tuntuɓeshi ta wayar salula.

Yace harin ya shafi wasu daga cikin motocin dake harabar wajen amma ginin hedkwatar ya tsira ba'a yi ɓanna a cikinsa ba.

KARANTA ANAN: Babbar Magana: Zama Gwamna Ƙara Talautad Dani Yayi, Inji Tsohon Gwamna

Yace: "An sanar da yan kwana-kwana jim kaɗan bayan harin kuma sun yi gaggawar zuwa wurin suka ƙashe wutar domin gujewa yaɗuwarta zuwa cikin ainihin ofishin."

Hakanan kuma, kwamishinan yan sandan jihar ya bada umarnin jibge jami'an tsaro a hedkwatar INEC ɗin domin tabbatar da tsaro a yankin.

A jawabin da kakakin hukumar yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya fitar, yace:

"A ranar Lahadi 16 ga watan Mayu, wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun yi ƙoƙarin ƙona hedkwatar hukumar INEC ta jihar Enugu, amma jami'an tsaro sun sami nasarar korar su."

"Hukumar kashe gobara ta jihar tayi namijin ƙoƙari wajen daƙile wutar a lokacin da ya dace domin kaucewa yaɗuwarta."

"Hakanan kuma, kwamishinan yan sandan jihar, Muhammad Aliyu, wanda yayi gaggawar zuwa wurin da lamarin ya faru, ya bada umarnin tsaurara tsaro a yankin."

A wani labarin kuma Ganduje Yayi Kira Ga Fulani Makiyayan Da Aka Hana Kiwo Su Dawo Jihar Kano

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya roƙi fulani makiyaya waɗanda dokar hana kiwo a kudu ta shafa su dawo jihar Kano.

Gwamnan yayi wannan kira ne yayin da ya tarbi sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a gidan gwamnatin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel