Matafiya Sun Shiga Mawuyacin Hali Sakamakon Yajin Aikin Kwadago a Jihar Kaduna
- Rahotanni sun bayyana cewa, matafiya sun shiga wani hali biyo bayan fara yajin aikin kungiyar NLC
- Kungiyar NLC ta tsunduma yajin aiki, lamarin da ya jawo rufe wajajen ayyuka da dama a Kaduna
- Matafiya a tashar jirgin kasa sun makale bayan sayen tikiti a tashar Rigasa amma babu hanyar tafiya
Wasu matafiya sun makale a tashar jirgin kasa ta Rigasa da ke Kaduna a ranar Litinin sakamakon yajin aikin da kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) ta tsunduma, Daily Trust ta ruwaito.
A makon da ya gabata, kungiyar kwadago ta NLC ta sha alwashin rufe tashar jirgin kasa, filin jirgin sama da sauran muhimman wurare a jihar kan abin da ta bayyana da manufofin yaki da kwadago daga Gwamnatin Jihar Kaduna.
Amma Gwamna Nasir El-Rufai ya ja kunnen kungiyar kwadago ta NLC, yana mai cewa gwamnatinsa na jiransu daram.
KU KARANTA: 'Yan Bindiga Basu Yi Wa 'Ya'yanmu Fyade Ba, Sun Kashe Mutuminsu Saboda 'Ya'yanmu
El-Rufai ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da aniyarta, yana mai jaddada cewa ba zai yiyuwa ba a kashe 84% zuwa 96% na kudaden da gwamnatin tarayya ke warewa kan albashi da kudaden ma'aikata.
Gwamnatin jihar ta lura cewa an yi mata kage tare da bata suna da kuma ikirarin karya cewa aikinta na take hakkin ma'aikata ya shafi ma'aikata 4,000 kuma ta daina biyan mafi karancin albashi.
A ranar Litinin, mambobin kungiyar kwadago ta NLC suka fara yajin aikin, tare da shan alwashin ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai gwamnatin Kaduna ta yi watsi da “manufofinta na kin jinin mutane”.
A Rigasa, an ga wasu matafiya da suka sayi tikiti a kan layi sun makale.
Amma an shaida musu tikitin cewa nasu zai ci gaba da aiki muddin suka yi amfani da su bayan da aka janye yajin aikin.
KU KARANTA: 'Yan Ta'addan IPOB Sun Kashe 'Yan Sanda 2, Sun Kona Ofishin 'Yan Sanda
A wani labarin, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) a jiya ta yi zargin cewa gwamnatin jihar Kaduna na shirin kutsa kai cikin zanga-zangarta tare da tura ‘yan daba, The Nation ta ruwaito.
Sanarwar ta ce an yaudaru ne wajen yaba wa gwamnatin Nasir El-Rufai saboda kasancewa ta farko da ta fara biyan sabon mafi karancin albashin N30,000.
NLC, a cikin wata sanarwa ta bakin Shugabanta na Majalisar Jihar Kaduna, Ayuba Suleiman, ya ce tun tunu jihar ta sake komawa ga tsohon tsarin albashin N18, 000 ga wasu ma’aikatan.
Asali: Legit.ng