'Yan Bindiga Basu Yi Wa 'Ya'yanmu Fyade Ba, Sun Kashe Mutuminsu Saboda 'Ya'yanmu
- Iyayen daliban Afaka da aka sako sun karyata jita-jitan dake cewa an aikata lalata da 'ya'yansu
- Hakazalika sun bayyana cewa, ya kamata mutane su yi watsi da jita-jitar domin kuwa karya ce
- Sun kuma bayyana cewa sun fi mai da hankali kan gyara 'ya'yansu da Allah ya dawo musu dasu
Iyayen daga cikin daliban da aka sace na Kwalejin Nona da Ilimin Gandun Daji ta Tarayya sun yi watsi da ikirarin da ke cewa an yi fyade ga ’ya’yansu ta hanyar lalata da luwadi a tsawon kwanaki 56 da suka kwashe a hannun 'yan bindiga.
Ku tuna cewa a ranar 11 ga watan Maris, 2021, 'yan bindiga sun mamaye kwalejin da ke Afaka a kan titin filin jirgin saman Kaduna suka sace dalibai 39.
Iyayen sun ce babu wani daga cikin ’ya’yansu (daliban) da 'yan bindigan suka yi lalata da su. 'Yan bindigan sun nemi a ba su N500m kudin fansa kafin su sake su.
KU KARANTA: Shugaba Buhari Ya Isa Kasar Faransa, An Bayyana Dalilan Zuwansa Taron
Iyayen daliban da aka sako sun bayyana cewa tunanin lalata da daliban da daya daga cikin 'yan bindigan yayi shine yasa aka harbe shi har lahira.
Wannan ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar Iyaye, Malam Abdullahi Usman ya fitar a Kaduna ranar Lahadi, a Rahoton Reuben Abati.
Sanarwar ta ce, “Mun bayyana karara cewa babu daya daga cikin 37 din da aka sace (wanda aka sako yanzu) na daliban Afaka da 'yan bindiga suka yi lalata da su ko kuma luwadi.
“Don tabbatarwa, daliban sun yi ikirarin cewa 'bai ma gwada hakan da gaske ba; yana fada ne kawai, amma duk da haka an kashe shi kuma an bukaci mu dauki gawarsa mu jefar a wani daji dake kusa saboda sun ce bai cancanci a binne shi yadda ya kamata ba.
“A matsayinmu na iyayen daliban da aka sako, babban abinda muka maida hankali a kai yanzu shi ne gyara 'ya'yanmu da Allah ya dawo mana da su a raye kuma abin mamaki ba a cutar da su ba.
KU KARANTA: Dawo-dawo: Matasan Najeriya Sun Kudiri Aniyar Tarawa Jonathan Kudin Takara a 2023
A wani labarin, Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, a ranar Lahadi ya karbi bakuncin daliban Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Tarayya dake Kaduna, wadanda kwanan nan suka samu 'yanci daga hannun 'yan bindiga.
A ranar 12 ga watan Maris, 'yan bindiga sun mamaye makarantar da ke kan titin filin jirgin sama a Kaduna suka yi awon gaba da dalibai 39.
An saki goma daga cikinsu bayan rahotanni sun nuna cewa iyayensu sun biya kudin fansa naira miliyan 17, TheCable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng