'Yan Ta'addan IPOB Sun Kashe 'Yan Sanda 2, Sun Kona Ofishin 'Yan Sanda

'Yan Ta'addan IPOB Sun Kashe 'Yan Sanda 2, Sun Kona Ofishin 'Yan Sanda

- Wasu dauke bindigogi da ake zargin tsagerun IPOB ne sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta a Abia

- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun hallaka 'yan sanda biyu a yayin harin da suka kawo

- Hare-hare kan kan ofisoshin gwamnati na ci gaba da faruwa a yankunan kudu maso gabashin Najeriya

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) sun kashe jami’ai biyu tare da kona wani ofishin ‘yan sanda a jihar Abia.

An kai harin ne kan Ofishin ‘yan sanda na Apumiri Ubakala da ke karamar hukumar Umuahia ta Kudu a jihar Abia da sanyin safiyar yau Litinin.

Ofishin da abin ya shafa yana cikin shahararriyar kasuwar Ubakala.

KU KARANTA: Shugaba Buhari Ya Isa Kasar Faransa, An Bayyana Dalilan Zuwansa Taron

Da Dumi-Dumi: 'Yan Ta'addan IPOB Sun Hallaka 'Yan Sanda 2, Kona Ofishin 'Yan Sanda
Da Dumi-Dumi: 'Yan Ta'addan IPOB Sun Hallaka 'Yan Sanda 2, Kona Ofishin 'Yan Sanda Hoto: pmexpressng.com
Asali: UGC

Wani jami’in dan sanda ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa kafin lamarin ya faru, rundunar ’yan sanda ta samu bayanan sirri na wani hari da ke gab da faruwa kuma an shawarce su da su rufe ofishin ko kuma su karfafa tsaro amma ba a yi hakan ba.

Wannan shi ne hari na baya-bayan nan da aka kai wa cibiyoyin gwamnati a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

An kai hari wani ofishin ‘yan sanda a jihar Enugu kwanan nan.

'Yan kwanaki da suka gabata, an yi kaca-kaca da Ofishin 'yan sanda na Bende a jihar Abia. Lamarin ya faru ne jim kadan bayan kai hari kan Ofishin ‘yan sanda na Uzuakoli, inda aka yi amfani da sinadarin dynamite da roka wajen kona ofishin da ke yankin.

An kai hari ofishin ‘yan sanda na Kasuwar Ubani mako guda da ya gabata yayin da aka yi kaca-kaca da ofishin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ke karamar Hukumar Ohafia na Abia a daren da ya gabata.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Basu Yi Wa 'Ya'yanmu Fyade Ba, Sun Kashe Mutuminsu Saboda 'Ya'yanmu

A wani labarin, A ranar Lahadin da ta gabata ne rundunar ‘yan sanda reshen jihar Imo ta ba da sanarwar cewa ta cafke wani dan sanda na bogi kuma dan bindiga, mai suna Michael Osundu.

A cewar kakakin rundunar, tare da Orlando Ikeokwu, an gano bindiga guda daya da harsasai 26, da kuma kakin ‘yan sanda guda biyu masu mukamin Mataimakin Sufeta Janar, wadanda aka boye su a cikin motarsa ​​kirar Toyota Escalade mai bakin gilashi.

Ikeokwu ya bayyana cewa ana zargin Osundu dan kungiyar 'yan daba ne da suka kai hari hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar da kuma gidan yari na Owerri a ranar 5 ga Afrilu, jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel