Shugaba Buhari Ya Isa Kasar Faransa, An Bayyana Dalilan Zuwansa Taron
- Shugaba Buhari ya isa kasar Faransa don tattauna wasu abubuwa masu muhimmancin gaske
- Shugaba Buhari zai kuma gana da shugaban kasar Faransa kan wasu batutuwa da aka bayyana
- Hakazalika zai gana da masu ruwa da tsaki na yankin turai kan batutuwa da suka shafi tattalin arziki
A jiya Lahadi 16 ga watan Mayu ne shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya shilla zuwa kasar Faransa don halartar taron tattauna kan tattalin arzikin kasashen Afrika.
Taron zai yi bitar tattalin arzikin Afirka, biyo bayan kaduwa daga annobar Korona da samun sauki, musamman daga karuwar bashin da ke kan kasashe, TheCable ta ruwaito.
A yayin ziyarar ta kwanaki hudu, Buhari zai kuma gana da Emmanuel Macron, shugaban Faransa.
KU KARANTA: An Kame Dan Sandan Bogi da Ake Kitsa Kone-konen Ofisoshin 'Yan Sanda Dashi
Ana sa ran Buhari da Macron za su tattauna kan barazanar tsaro da ke ci gaba da addabar yankin Sahel da Tafkin Chadi, canjin yanayi, alakar tattalin arziki, alakar siyasa, kawance don inganta bangaren kiwon lafiyar Najeriya da kuma dakile yaduwar Korona.
A wata sanarwa a ranar Asabar, fadar shugaban kasar ta ce taron zai kuma “mai da hankali kan nazarin tattalin arzikin Afirka, biyo bayan damuwa daga cutar Korona da kuma samun sauki, musamman daga karin bashin da ke kan kasashen.”
"Kafin ya dawo Najeriya, Shugaba Buhari zai karbi wasu manyan masu ruwa da tsaki a bangaren man fetur da iskar gas, injiniyanci da sadarwa, Majalisar Tarayyar Turai da Wakilin Tarayyar Turai kan Harkokin Kasashen Waje da Tsaro, da kuma mambobin al'ummar Najeriya."
Ana sa ran manyan masu ruwa da tsaki a cibiyoyin kudi na duniya da wasu shugabannin gwamnatoci za su halarci taron.
Hakazalika, Legit.ng Hausa ta gano wata sanarawa da mataimakin shugaba Buhari na musamman kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad tana cewa:
"Shugaba Buhari ya isa birnin Paris na Faransa gabanin taron kolin kudi na Afirka wanda zai mayar da hankali kan nazarin tattalin arzikin Afirka. #PMBinParis"
KU KARANTA: NLC: Tuni El-Rufai Ya Koma Biyan N18,000 a Matsayin Mafi Karancin Albashi
A wani labarin, Wata kungiya karkashin inuwar kungiyar matasa mai suna 'Earnestly Demand For Goodluck E.Jonathan' (YED4GEJ 2023) ta nemi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da ya sake fitowa takarar shugaban kasa a 2023.
Jonathan ya rasa mulki ne a zaben shekarar 2015, wanda hakan ya kawo karshen shekaru 16 na mulkin Jam’iyyar PDP a kasar, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kungiyar na kasa, Prince Teddy Omiloli da Daraktan Ayyuka na kasa na kungiyar, Kwamared Douye Daniel a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi sun nuna kwarin gwiwa cewa Jonathan zai magance kalubalen da ke addabar kasar idan aka ba shi dama.
Asali: Legit.ng