Jarumi Lawan Ahmad ya zabgawa jaruma mai tasowa mugun mari a wurin shirya fim
- Jarumin Kannywood, Lawan Ahmad ya zabgawa jaruma Hannatu Usman mugun mari
- Lamarin ya faru ne a Kano inda ake daukar shirin Bugun Zuciyar Masoya kashi na 37
- Yunkurin cire jarumar ne ya fusatata har ya kai ga jarumin ya zageta sannan ya zabga mata mari
Akwai zargin cewa ran jarumi Lawan Ahmad yayin da ya zabgawa jaruma Hannatu Usman mari yayin da ake wurin daukar fim mai dogon zango mai suna 'Bugun Zuciyar Masoya'.
Lamarin ya faru ne a Kano yayin da ake shirye-shiryen daukar shirin kashi na 37 wanda jarumar ke fitowa da suna Nafisa.
Wata majiya mai karfi ta sanar da mujallar fim cewa ran Hannatu ya kai matuka a baci bayan an sanar da ita cewa labarin baya bukatarta kuma za a sauyata da wata jaruma saboda hadari da tayi a fim din.
Majiyar da ta bukaci a rufa sunanta, ta bada tabbacin samun matsalar.
"Kowanne fim ana yin shi ne domin ruba kuma shirin dirama mai dogon zango ta gaji hakan. Ana iya cire mutum idan aka ga dama ko kuma labarin baya bukatar mutum."
KU KARANTA: Da duminsa: Sojin Najeriya sun cafke Jack Bros Yellow, shugaban 'yan bindigan Neja
KU KARANTA: Da duminsa: JAMB ta bada sabuwar muhimmiyar sanarwa kan jarabawar UTME ta 2021
Kamar yadda majiyar tace, "An san Lawan Ahmad da zafi kuma a tunanin jarumar ba za a iya yin shirin fim din babu ita. Bayan sanar da ita za a cireta, sai ta fara wasu maganganu marasa dadi wadanda suka kai ta da samun rashin jituwa da Darakta Nura Mustapha Waye.
"Lawan Ahmad ya tsoma baki tare da zagin Hannatu har abu ya kai ga mari."
An so jin ta bakin jaruma Hannatu Usman kan lamarin amma abun ya gagara saboda ba sameta ta waya ba.
Amma an samu jarumi Lawan Ahmad da ake zargi da marin jarumar inda a take ya musanta hakan tare da cewa bai san lokacin da lamarin ya faru ba.
A wani labari na nan, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugaban kasan rikon kwarya na soji na kasar Chadi, Laftanal Janar Mahamat Idris Deby Itno da kada su yi kasa a guiwa wurin neman taimako daga Najeriya a duk lokacin da suke bukatar hakan.
Shugaban kasan ya kara da daukan alkawarin cewa zai taimaki jamhuriyar Chadi wurin samun daidaito da kuma komawa kundun tsarin Mulki.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da hakan ne a ranar Litinin yayin da ya karba bakuncin Janar Deby Itno a fadarsa dake Aso Villa, Abuja.
Asali: Legit.ng