Bauchi: Sarki ya dakatar da Wakilin Birni saboda zarta shi walkiya yayin hawan sallah

Bauchi: Sarki ya dakatar da Wakilin Birni saboda zarta shi walkiya yayin hawan sallah

- Sarkin Rilwanu Sulaiman Adamu na jihar Bauchi ya dakatar da Wakilin Birnin Bauchi, Yakubu Shehu Abdullahi, bayan hawan sallah

- An gano cewa Sarkin yayi haka ne saboda tsabar adon da mai sarautar ya caba cikin Alkyabba da Kandiri, wacce ta zarta ta sarkin

- Duk da dai a wasikar dakatarwan an sanar da cewa an dade ana ja wa Wakilin Birni kunne, ya ki gaida Gwamna yayin hawan sallah

Sarkin Bauchi, Rilwanu Sulaiman Adamu, ya dakatar da Wakilin Birnin Bauchi, Yakubu Shehu Abdullahi, a kan rashin da'a ga sarki da kuma shigar alfarmar da yayi tamkar Sarki yayin hawan Sallah.

Masarautar tace Abdullahi, wanda dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Bauchi a tarayya karkashin jam'iyyar PRP, an dade ana jan masa kunne a kan rashin da'a ga sarki da masarautar amma yayi kunnen kashi.

A wata wasika mai kwanan wata 16 ga Mayun 2021 wacce aka aika ga dan majalisar a harshen Hausa, masarautar tace shigar da yayi a Alkyabba da Kandiri a gaban sarki ba al'amari bane na da'a.

KU KARANTA: Kada ku yi kasa guiwa wurin neman taimako daga Najeriya, Buhari ga Shugaban Chadi

Bauchi: Sarki ya dakatar da Wakilin Birni saboda zarta shi walkiya yayin hawan sallah
Bauchi: Sarki ya dakatar da Wakilin Birni saboda zarta shi walkiya yayin hawan sallah. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rashin tsaro: Lalong ya bayyana abinda marigayi Dogonyaro ya sanar da shi

"Masarautar karkashin shugabancin Sarkin Bauchi, ta duba ayyukanka wanda ta ga rashin da'a ne ga Sarki, shugabannin siyasa, 'yan majalisar sarki, hakimai da sarakuna.

“Masarautar ta bada misali da yadda ka bayyana gaban Sarakuna da Alkyabba da Kandiri duk da an ja maka kunne a kan hakan.

“Abinda ya faru a ranar Asabar, 15 ga watan Mayun 2021 a gidan gwamnati ya nuna yadda baka da'a ga Sarki, masu sarauta da gwamna.

"A saboda haka, masarautar ta dakatar da kai daga sarautar Wakilin Birnin Bauchi har sai baba ta gani," wasikar tace.

An gano cewa dan majalisar wanda ya bayyana a hawan sallah tare da mukarrabansa cikin shigar alfarma, ya ki gaishe da Gwamna bayan gaida Sarki da yayi.

A wani labari na daban, 'yan bindigan da suka dade suna addabar yankuna daban-daban na kasar nan sun ce suna samun makamai ne daga jami'an hukumar tsaro ta farin kaya kuma su kan raba kudin fansa tare ne idan sun karba.

'Yan ta'addan sun sanar da Deutsche Welle a wani rahoto da suka fitar na cewa suna aron makamai ne daga jami'an tsaro farin kaya kuma suna raba kudin da suka samu, Vanguard ta wallafa.

'Yan ta'addan sun kara da cewa wasu daga cikin jami'an 'yan sanda na daga cikin wadanda suke hada kai dasu wurin assasa wutar rashin tsaro a kasar nan wanda kuma ake zargin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasa shawo kai.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel