'Yan Najeriya ne ke ta rokona in fito takarar shugabancin kasa, Yahaya Bello

'Yan Najeriya ne ke ta rokona in fito takarar shugabancin kasa, Yahaya Bello

- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello yace dukkan 'yan Najeriya ne ke ta rokonsa da ya fito takarar shugabancin kasa a 2023

- Gwamnan yace babu shakka akwai abinda mata da matasa suka hango a tare da shi ne, shiyasa suke ta wannan tururuwar garesa

- A cewarsa, kasar Najeriya tana bukatar tsayayyen mutum da zai iya hada kan jama'a, kuma babu shakka zai iya hakan

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya ce "dukkan 'yan Najeriya" ne suke bukatarsa da ya nemi kujerar shugabancin kasa a zaben 2023 mai zuwa.

A yayin jawabi a ranar Juma'a yayin da ake yin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels, Bello ya ce zai bada ansa ga wannan bukatar nan babu dadewa.

Gwamnan yace 'yan Najeriya suna bukatar dan takara da zai hada kan kasar nan, kuma ya yadda yana da dukkan nagartar da ake bukata domin zama shugaban kasa.

KU KARANTA: Buhari ya sha alwashin daukan mataki kan 'yan bindiga, barazana ga rashin abinci

'Yan Najeriya ne ke ta rokona in fito takarar shugabancin kasa, Yahaya Bello
'Yan Najeriya ne ke ta rokona in fito takarar shugabancin kasa, Yahaya Bello. Hoto daga @TheCableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Sojin Najeriya sun cafke Jack Bros Yellow, shugaban 'yan bindigan Neja

"Matasa da mata tare da dukkan 'yan Najeriya suke rokona da in tsaya takarar shugaban kasa a 2023. Kuma na yadda cewa lokaci yayi da zan duba ko zan iya. Waye zai iya hada kan kasar nan? Ina tunanin suna ganin wani abu a tare da ni ne shiyasa suke son in zo in hada kan kasar nan kuma in gyarata," yace.

"Nan babu dadewa zan ansa musu. Ina kira ga kowa da kowa dake yi min wannan kiran na takarar shugabancin kasa da su yi hakuri.

"Har yanzu akwai aikin da nake kuma da izinin Ubangiji, ba zan baku kunya ba idan lokacin yanke hukuncin zan fito takara ko ba zan fito ba yayi."

A wani labari na daban, hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare (JAMB) ta fara magana a kan yuwuwar sauya lokacin rubuta jarabawar na shekarar 2021.

Dama za a rubuta jarabawar ne daga ranar 6 ga watan Yunin 2021 zuwa ranar 19 ga watan Yunin 2021.

Hukumar shirya jarabawar amma ta tabbatar da cewa za a rubuta jarabawar gwajinta a ranar 20 ga watan Mayun 2021 bayan sauya ranar da tayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng