Sheikh Gumi Ya Gana da Daliban Kwalejin Afaka, Ya Bayyana Yadda Ya Taimaka Aka Sako Su

Sheikh Gumi Ya Gana da Daliban Kwalejin Afaka, Ya Bayyana Yadda Ya Taimaka Aka Sako Su

- Shararren malamin addinin Islama, Gumi ya bayyana yadda ya taimaka aka ceto daliban Afaka

- A cewarsa, an yi amfani da ilimin halayyar dan adam wajen shawo kan 'yan bindiga suka sako su

- Ya kuma bukaci gwamnati da ta hada kai wajen tattaunawa da 'yan bindigan don magance matsalar tsaro

Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, a ranar Lahadi ya karbi bakuncin daliban Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta Tarayya dake Kaduna, wadanda kwanan nan suka samu 'yanci daga hannun 'yan bindiga.

A ranar 12 ga watan Maris, 'yan bindiga sun mamaye makarantar da ke kan titin filin jirgin sama a Kaduna suka yi awon gaba da dalibai 39.

An saki goma daga cikinsu bayan rahotanni sun nuna cewa iyayensu sun biya kudin fansa naira miliyan 17, TheCable ta ruwaito.

Ragowar daliban 29 sun samun 'yanci a ranar 5 ga watan Mayu bayan sun kwashe kwanaki 54 a tsare.

Gumi da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo an ce sun taimaka wajen saukaka sakin nasu.

KU KARANTA: Yunwa Ta Kusa Zarce Boko Haram da 'Yan Bindiga Kisa a Najeriya, Jigo a PDP

Sheikh Gumi Ya Gana da Daliban Afaka, Ya Bayyana Yadda Ya Taimaka Aka Ceto Su
Sheikh Gumi Ya Gana da Daliban Afaka, Ya Bayyana Yadda Ya Taimaka Aka Ceto Su Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Da yake jawabi a yayin wani taro a Dakin taro na Masallacin Sultan Bello, Gumi ya bukaci daliban da su mance da abubuwan da suka gabata.

Da aka tambaye shi yadda ya samu nasarar sakin daliban, Gumi ya ce: “Ba a sasantawa da aboki, ana sasantawa ne da makiyi.

Sheikh Gumi Ya Gana da Daliban Afaka, Ya Bayyana Yadda Ya Taimaka Aka Ceto Su
Sheikh Gumi Ya Gana da Daliban Afaka, Ya Bayyana Yadda Ya Taimaka Aka Ceto Su Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

“Abu na farko da za ku yi shi ne, kokarin gwada kankara da karya shingen da ke tsakaninku da wanda kuke tattaunawa da shi da kuma kara karfin gwiwa ta hanyar nuna cewa ba za ku cucesu ba ko kuma ku yaudaresu.

“Idan akwai wannan matakin na sadarwa, to tattaunawa ta zo a kashi na uku.

“Wadannan mutane ne da suka dade suna irin wannan laifin, dole ne mu yi amfani da ilimin halayyar dan adam a kansu saboda ba zai yiwu a dare daya kawai su sauya ba.

"Amma yi musu wa'azi, tunatar da su da kuma nuna musu hanyar fita daga matsalolinsu ya taimaka matuka wajen sanya su fahimta da sakin wadannan yaran."

Malamin ya yi kira ga hadin kan gwamnatoci a dukkan matakai don magance matsalolin tsaro da ke addabar kasar.

Sheikh Gumi Ya Gana da Daliban Afaka, Ya Bayyana Yadda Ya Taimaka Aka Ceto Su
Sheikh Gumi Ya Gana da Daliban Afaka, Ya Bayyana Yadda Ya Taimaka Aka Ceto Su Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

"Rokona ga gwamnati shi ne ta yi hulda da 'yan bindigan don su watsar da halayyarsu," in ji shi.

“Tuni suna nuna alamun cewa sun shirya. Suna da korafe-korafe, wanda nake ganin idan muka taru za mu iya magance wannan matsalar a cikin kankanin lokaci.”

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Malamin Addini Tare da Mutane 2 Nasarawa

A wani labarin, Bayan ingantattun bayanan sirri, sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai sun yi ruwan bama-bamai kan tarin mayakan Boko Haram a kauyen Dawuri da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

Jaridar PRNigeria ta tattaro cewa 'yan ta’addan suna shirin kai hare-hare ne a kewayen Maiduguri lokacin da Sojojin Najeriya suka kai hari da manyan bindigogi a sansaninsu.

Wani jami’in leken asirin soja da ke cikin aikin ya fada cewa sojojin sun fara kai hare-haren ne bayan da suka samu bayanan sirri kan motsin mayakan da kuma kutse ta hanyar sadarwar su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.