Hana Kiwo: Ganduje Yayi Kira Ga Fulani Makiyayan Da Aka Hana Kiwo Su Dawo Jihar Kano

Hana Kiwo: Ganduje Yayi Kira Ga Fulani Makiyayan Da Aka Hana Kiwo Su Dawo Jihar Kano

- Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Ganduje, yayi kira ga makiyayan dake yankin kudu su dawo jihar Kano

- Gwamnan yayi wannan kira ne yayin da ya tarbi sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a gidan gwamnatin jihar

- Yace bai kamata gwamnonin kudancin ƙasar nan su ɗauki matakin hana kiwo ba, domin suma fulani yan Najeriya ne kamar kowa

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya roƙi fulani makiyaya waɗanda dokar hana kiwo a kudu ta shafa su dawo jihar Kano, kamar yadda leadership ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Kotu Ta Yankewa Musulmi 29 Hukuncin Kisa Saboda Rikici Kan Limancin Sallar Idi

Gwamnan yayi wannan jawabi ne yayin da ya tarbi sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, a gidan gwamnatin jihar.

Ganduje ya nuna damuwarsa bisa hana makiyaya kiwo da gwamnoni 17 na kudancin ƙasar nan suka yi.

Hana Kiwo: Ganduje Yayi Kira Ga Fulani Makiyayan su dawo jihar Kano
Hana Kiwo: Ganduje Yayi Kira Ga Fulani Makiyayan su dawo jihar Kano Hoto: @GovUmarGanduje
Asali: Twitter

Gwamnan yace:

"Gaskiya ne tsohon yayin da ake amfani da shi wajen kiwata dabbobi daga wani wuri zuwa wani wuri yana jawo talauci, amma idan ka duba yadda ake wa makiyaya a yankin kudu ba sai an faɗa maka irin wahalar da suke fuskanta ba."

"Ana ƙuntata wa fulani a yankin, ba zamu amince da haka ba kuma ya kamata a canza saboda suma dai-dai suke da kowane ɗan Najeriya, suna da yancin rayuwa a ko ina a Najeriya."

Ganduje yayi kira ga fulani makiyaya waɗanda abun ya shafa da su dawo jihar Kano, inda ya ƙara da cewa akwai wurin da aka ware musu na kiwon dabbobi a dajin Dansoshiya na jihar Kano.

KARANTA ANAN: Babu Makawa Sai Mun Hana Fulani Makiyaya Kiwo a Yankin Mu, Inji Gwamnan PDP

Gwamnan yace a koda yaushe jiharsa na maraba da baƙi kuma zata cigaba da basu kulawa yadda ya kamata.

A cewarsa ya kamata suma fulani a rinƙa basu kulawa yadda ya kamata a duk inda suka je a faɗin ƙasar nan.

A ɓangaren ƙalubalen tsaro kuma, gwamna Ganduje yace bai kamata a bar komai a hannun shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba saboda wannan aiki ne da ya rataya a wuyan kowa.

Ya ƙara da cewa ya zama wajibi a haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen ganin a dawo da zaman lafiya a ƙasar nan.

A wani labarin kuma Kamfanin Wutar Lantarki Ya Katse Duka Layukan Wutar Jihar Kaduna

Kamfanin wutar lantarki na jihar Kaduna TCN, ya katse duka layukan rarraba wutar lantarkin dake jihar domin bin umarnin ƙungiyar ƙwadugo.

Kamfanin yace ya zama waji ya yanke wutar kasan cewar dukkan ma'aikatansa na ƙarƙashin kungiyar ta NLC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel