Kotu Ta Yankewa Musulmi 29 Hukuncin Kisa Saboda Rikici Kan Limancin Sallar Idi

Kotu Ta Yankewa Musulmi 29 Hukuncin Kisa Saboda Rikici Kan Limancin Sallar Idi

- Musulmi 29 ne aka yanke wa hukuncin kisa a jamhuriyar demokaraɗiyyar Kongo saboda rikici a filin sallar Idi

- A yayin rikin tsakanin ƙungiyoyin musulmi biyu, jami'in ɗan sanda ɗaya ya rasa rayuwarsa tare da jikkata wasu da dama

- Kafin ranar Idi, shugabannnin ƙungiyoyin biyu sun tabbatarwa da hukumomi za'a yi sallah lami-lafiya amma hakan bata faru ba

Musulmi 29 zasu fuskanci hukuncin kisa saboda rikicin da ya faru a filin idi ranar Alhamis a jamhuriyar demokaraɗiyyar Kongo.

KARANTA ANAN: Babu Makawa Sai Mun Hana Fulani Makiyaya Kiwo a Yankin Mu, Inji Gwamnan PDP

Rikicin dai yayi sanadiyyar mutuwar jami'in ɗan sanda tare da jikkata wasu da dama, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Rikicin ya ɓarke ne ranar idi a Kinshasha, Babban birnin Kongo tsakanin ɓangarorin musulmi biyu kan waye ya dace ya jagoranci sallar idi bayan kammala azumin watan Ramadana.

Kotu Ta Yankewa Musulmi 29 Hukuncin Kisa Saboda Rikici Kan Limancin Sallar Idi
Kotu Ta Yankewa Musulmi 29 Hukuncin Kisa Saboda Rikici Kan Limancin Sallar Idi Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Yayin rikicin wanda yayi sanadiyyar ƙona motar yan sanda, jami'an tsaro sun yi nasarar damƙe mutane 40 da aka gurfanar dasu a gaban shari'a.

An kuma gudanar da shari'ar a bayyane, inda aka rinƙa nuna ta kai tsaye a kafar Talabishin duk tsawon dare.

Sai-dai kasan cewar a yanzun ba'a aiwatar da hukuncin kisa a ƙasar ta Kongo, a maimakon haka mutanen zasu yi zaman gidan gyaran hali na tsawon shekaru masu yawa.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Jami’an Tsaro Sun Harbe Yan Bindiga Huɗu Tare da Ma’aikaciyar Jinya

Rahotanni sun tabbatar da cewa a yayin rikicin da ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin musulmai biyu, wani ɗan sanda ya rasa rayuwarsa, wasu da dama sun jikkata.

Daman akwai Saɓani tsakanin manyan ƙungiyoyin biyu a jamhuriyar Kongo kan wanda zai zama jagoran al'ummar musulmi.

Tun kafin ranar sallar idi, shugabannin ƙungiyoyin biyu sun tabbatar wa da hukumomi zasu gudanar da salla cikin kwanciyar hankali.

Kusan kashi 10% na al'umar Kinshasha mabiya addinin musulunci ne kuma mafi yawancin su suna yankin gabashi ne.

A wani labarin kuma Masallatan da Aka sace Daga masallacin Katsina Sun Samu Yanci

Rahoto ya nuna cewa mutane 11 cikin wadanda yan bindiga suka sace a masallacin Jibiya da ke jihar Katsina sun samu yanci.

Hakan ya kasance ne da taimakon matar daya daga cikin yan fashin da suka sace su, inda ta kwance su sannan ta nemi su tsere.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262