Yunwa Ta Kusa Zarce Boko Haram da 'Yan Bindiga Kisa a Najeriya, Jigo a PDP

Yunwa Ta Kusa Zarce Boko Haram da 'Yan Bindiga Kisa a Najeriya, Jigo a PDP

- Jigo a jam'iyyar PDP ya koka kan yadda lamarin tsaro ke son illata 'yan Najeriya nan gaba

- Ya bayyana cewa, yunwa za ta fi Boko Haram da 'yan bindiga barna nan kusa ba da jimawa ba

- Ya kuma bukaci gwamnatin APC da ta gaggauta daukar mataki ba tare da bata lokaci ba

Tsohon Mataimakin Shugaban Jam'iyyar PDP na kasa, Dr Eddie Olafeso, ya yi magana kan matsalar tsaro da ta dabaibaye Najeriya.

Olafeso ya bayyana yadda anan gaba yunwa za ta zama wata abar tsoro a Najeriya sakamakon tabarbarewar tsaro.

A cewarsa, cikin wata hira da jaridar Punch wacce Legit.ng Hausa ta gano, dukkan masu jigilar ayyukan samar da abinci a tsorace suke, saboda haka samar da abinci ya zama wani halin wayyo Allah a Najeriya.

KU KARANTA: Isra'ila Ta Yi Kaca-kaca da Gidan Jagoran Hamas a Yankin Zirin Gaza

Yunwa Ta Kusa Zarce Boko Haram da 'Yan Bindiga Kisa a Najeriya, Jigo a PDP
Yunwa Ta Kusa Zarce Boko Haram da 'Yan Bindiga Kisa a Najeriya, Jigo a PDP Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Ya ce: "Dalilin karancin abinci a bayyane yake. Tun daga wannan lokacin manoma sun yi watsi da gonakinsu saboda rashin tsaro. Masunta ba za su iya zuwa kamun kifi ba saboda tsoron sace su.

"Mu da muke kiwon tsuntsayen gida ba za mu iya yin haka ba saboda abincinsu ya yi tsada sosai. An lalata gonaki ba tare da hukunci ba, an sace manoma, an yi musu fyade, wasu sun nakasa wasu an kashe su.

Ya kuma koka kan yadda gwamnatin jam'iyyar APC ta gagara daukar mataki kan lamurran tsaro a Najeriya, yana mai bayyana tsoronsa a nan gaba cewa yunwa za ta zarce Boko Haram, 'yan bindiga da ma cutar Korona a kisa.

"To menene na gaba? Yunwa ita ce mataki na gaba da gwamnatin APC tayi alkawari. Yunwa tana mutukar kisa. Za ta iya kashe mutane fiye da Boko Haram, masu satar mutane da ma Korona.

"Yawancin 'yan Najeriya suna cikin tsananin yunwa, ba su da abin da za su ci. Ba a taba shiga irin wannan mummunan halin ba.

"Wadanda kuke tsammanin suna lafiya ba sa cikin kwanciyar hankali ko kadan. Abu ne mai ban tsoro kuma akwai tsananin bukatar a yi wani abu akai. Abin takaici ne matuka cewa a cikin yalwar ruwa, wawa yana jin kishirwa.

KU KARANTA: Gini Ya Ruguje Tare da Kashe Uwa da 'Ya'yanta 4 a Gaza , An Yi Nasarar Ceto Jaririnta

A wani labarin daban, An rahoto cewa an sace wani Sufeto Janar na Kwastam, Mba Ukweni Edu da yammacin ranar Juma'a da Ferry Point a yankin Eton Central na Biakpan dake Jihar Kuros Riba.

Jaridar Sunday Tribune ta tattaro cewa lamarin ya faru ne tsakanin karfe 1.00 na rana zuwa 2.00 na yamma, lokacin da wanda aka sacen da aka tura kwanan nan zuwa yankin Ikom, ya dawo Calabar daga sansaninsa.

Ukweni, wanda aka ce dan kawu ne ga masanin dokoki, Mba Ukweni, Babban Lauyan Najeriya (SAN), zai yi ritaya nan ba da jimawa ba, saboda an yi imanin cewa sabon mukamin nasa na shirye-shiryen ritayar ne.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel