'Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Malamin Addini Tare da Mutane 2 Nasarawa

'Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Malamin Addini Tare da Mutane 2 Nasarawa

- Wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun afkawa wasu mutane, sun kashe mutum 3

- An ruwaito cewa, sun kashe wani malamin addinin kirista tare da wasu mutane biyu a yankin

- Mutanen yankin sun fara tattara kayayyakinsu suna barin yankin saboda yawan hare-hare

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kashe wani malamin addinin kirista mai suna Sydney Shirsha da wasu mutum biyu a kauyen Amudu da ke Giza a masarautar karamar Hukumar Keana ta Jihar Nasarawa.

Daily Trust a ranar Lahadi ta gano cewa ’yan bindigan da ake zargi, wadanda ke dauke da muggan makamai, sun afka wa Amudu, wani kauyen kabilar Tiv da ke yankin Giza, a tsakar daren Asabar.

Karin bayanin da aka samu ya nuna cewa harin ya bar wasu da dama da raunuka daban-daban na harbin bindiga.

KU KARANTA: Hotunan Zulum da Oshiomole Na Yakin Neman Shugaban Kasa a 2023 Sun Bazu a Gombe

'Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Malamin Addini Tare da Mutane 2 Nasarawa
'Yan Bindiga Sun Hallaka Wani Malamin Addini Tare da Mutane 2 Nasarawa Hoto: aa.com.tr
Asali: UGC

An samu labarin cewa daruruwan mazauna yankin sun tsere daga yankin sakamakon harin.

Shugaban kungiyar Tiv Development Association (TIDA) a jihar Nasarawa, Kwamared Peter Ahemba, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya koka kan yadda ake ci gaba da kai hare-hare a kan mutanen sa.

Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar, ASP Rahman Nansel, ya ce har yanzu rundunar ba ta karbi wani rahoto na harin ba.

KU KARANTA: Bayan Kashe Dan Sanda da Kwace Bindigarsa, An Kame Tsagerun IPOB 6 a Jihar Imo

A wani labarin, An rahoto cewa an sace wani Sufeto Janar na Kwastam, Mba Ukweni Edu da yammacin ranar Juma'a da Ferry Point a yankin Eton Central na Biakpan dake Jihar Kuros Riba.

Jaridar Sunday Tribune ta tattaro cewa lamarin ya faru ne tsakanin karfe 1.00 na rana zuwa 2.00 na yamma, lokacin da wanda aka sacen da aka tura kwanan nan zuwa yankin Ikom, ya dawo Calabar daga sansaninsa.

Ukweni, wanda aka ce dan kawu ne ga masanin dokoki, Mba Ukweni, Babban Lauyan Najeriya (SAN), zai yi ritaya nan ba da jimawa ba, saboda an yi imanin cewa sabon mukamin nasa na shirye-shiryen ritayar ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel