Yan Bindiga Sun Sake Ƙone Wani Ofishin Yan Sanda, Jami’ai Uku Sun Rigamu Gidan Gaskiya

Yan Bindiga Sun Sake Ƙone Wani Ofishin Yan Sanda, Jami’ai Uku Sun Rigamu Gidan Gaskiya

- Wasu yan bindiga sun sake kai hari kan jami'an hukumar yan sanda a ƙaramar hukumar Aniocha dake jihar Delta da sanyin safiyar yau Lahadi.

- Ana tsammanin jami'an tsaron hukumar yan sanda uku ne suka rigamu gidan gaskiya yayin harin da aka kai musu

- Rahoto ya tabbatar da cewa maharan sun ƙone ginin ofishin tare da motocin su, yayin da suka yi awon gaba da wasu makamai

Wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun sake kai wani sabon hari kan jami'an hukumar yan sanda a jihar Delta, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Kotu Ta Yankewa Musulmi 29 Hukuncin Kisa Saboda Rikici Kan Limancin Sallar Idi

A yayin harin, yan bindigan sun ƙone ofishin yan sanda dake garin Nsukwa ƙaramar hukumar Aniocha ta kudu, jihar Delta, inda ake tsammanin jami'an yan sanda uku sun rigamu gidan gaskiya.

Rahoto ya bayyana cewa yan bindigan sun kai wannan mummunan harin ne da misalin ƙarfe 2:00 na safiyar yau Lahadi.

Yan Bindiga Sun Sake Ƙone Wani Ofishin Yan Sanda, Jami’ai Uku Sun Rigamu Gidan Gaskiya
Yan Bindiga Sun Sake Ƙone Wani Ofishin Yan Sanda, Jami’ai Uku Sun Rigamu Gidan Gaskiya Hoto: punchng.com
Asali: UGC

An gano cewa maharan sun ƙone ginin ofishin yan sandan da kuma motocin sintirin su sannan suka yi awon gaba da wasu makamai.

KARANTA ANAN: Rahoto Na Musamman: Yadda Jami’an Kwastam Suka Buɗe Wuta Ranar Sallah, Mutum 6 Suka Mutu

Mai magana da yawun hukumar yan sanda reshen jihar Delta, DSP Bright Edafe, bai samu damar ɗaga kiran wayar da aka masa ba domin jin tabbaci daga bakin hukumarsu.

Amma wata majiya a hukumar ta yan sanda dake Ogwash-Uku, maƙwaftan garin da lamarin ya faru ta tabbatar da kai harin.

Yan bindiga na cigaba da kai hari kan jami'an yan sanda da kuma kayan aikin su musamman a yankin kudancin ƙasar nan.

Hukumomi sun bayyana cewa suna iya bakin ƙoƙarin su wajen ganin an magance irin waɗannan hare-haren da yan bindiga ke kaiwa jami'an tsaro.

A wani labarin kuma Babu Makawa Sai Mun Hana Fulani Makiyaya Kiwo a Yankin Mu, Inji Gwamnan PDP

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike , ya bayyana matsayar da ƙungiyar gwamnonin kudu suka yanke ta hana kiwo da ba gudu ba ja da baya.

Gwamnan ya jaddada cewa babu wnda zai sa gwamnonin su fasa zartar da hukuncin da gaba dayansu suka amince da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel