Bayan Kashe Dan Sanda da Kwace Bindigarsa, An Kame Tsagerun IPOB 6 a Jihar Imo

Bayan Kashe Dan Sanda da Kwace Bindigarsa, An Kame Tsagerun IPOB 6 a Jihar Imo

- Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar kame wasu 'yan ta'addan kungiyar IPOB a jihar Imo

- An kama su da zargin hallaka wani jami'in dan sanda tare da yin awon gaba da makaminsa

- Tuni aka fara gudanar da bincike, ana kuma kokarin gurfanar dasu a gaban kotu nan kusa

Jami'an rundunar 'yan sanda reshen jihar Imo sun kame wasu mambobi shida na kungiyar tsagerun Biafra ta IPOB kan mutuwar wani jami'in dan sanda, Daily Trust ta ruwaito.

Ana zargin wadanda aka kamen da kashe Sgt Joseph Nwaka tare da yin awon gaba da makaminsa.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Orlando Ikeokwu ya fitar, ya ce an kwato bindiga kirar AK47 guda daya, bindigogi kiran gida guda hudu da kuma tabar wiwi da yawa daga hannunsu.

Ya bayyana sunan shugabansu a matsayin Onyeyekachi Maduforo, dan asalin Umudururkwe a karamar hukumar Isu.

KU KARANTA: Tabbatar da Tsaro a Bikin Sallah: An Jibge ’Yan Sanda Sama da 4000 a Jihar Kano

Bayan Kashe Dan Sanda da Kwace Bindigarsa, An Kame Tsagerun IPOB 6 a Jihar Imo
Bayan Kashe Dan Sanda da Kwace Bindigarsa, An Kame Tsagerun IPOB 6 a Jihar Imo Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

“A matsayin bin bahasi, a ranar 14 ga Mayu, 2021, Kwamishinan 'yan sanda ya tura sashin yaki da satar mutane da sauran tawaga na rundunar zuwa karamar hukumar Amanato Isu don kamo sauran mambobin kungiyar kuma sun yi musayar wuta da su 'yan ta'addan (IPOB/ESN).

“Jami’an sun yi nasarar fatattakarsu tare da tarwatsasu.

“Sakamakon arangamar, an cafke mutum biyar da ake zargi a wurin, yayin da wasu suka tsere da yiwuwar harbin bindiga.

“A yayin aikin, an gano muggan makamai guda hudu, harsasai shida da kuma ganye da yawa da ake zargin tabar wiwi ne.

Ya ce an fara gudanar da bincike da nufin ci gaba da kamun bayan haka za a gurfanar da su a gaban kotu.

KU KARANTA: Hotunan Zulum da Oshiomole Na Yakin Neman Shugaban Kasa a 2023 Sun Bazu a Gombe

A wani labarin, An rahoto cewa shanu sama da 12 sun mutu biyo bayan bugun tsawa a garin Urhodo-Ovu na karamar hukumar Ethiope East na jihar Delta, The Nation ta ruwaito.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, makiyayan suna zaune kusa da shanun yayin da aka dauke wasu daga ciki zuwa wani yanki na daji don kiwo lokacin da tsawar ta fado kan shanu sha biyu.

Majiyar ta yi bayanin cewa tsawar ta fado wa shanun ne bayan an dan yi ruwan sama, inda ta kara da cewa 'yan mintoci kadan sai shanun suka fadi matattu saboda cikinsu ya kumbura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel