Bayan Ruwan Sama, Tsawa Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Shanu Sama da 12 a Delta

Bayan Ruwan Sama, Tsawa Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Shanu Sama da 12 a Delta

- Biyo bayan ruwan sama, shanu sama da 12 sun mutu a jihar Delta, lamarin da ya jawo kaduwa

- Wasu mazauna sun bayyana yadda suka ji, sun kuma bayyana gargadin da aka yiwa makiyaya

- An rahoto cewa, manoma sun gargadi makiyayan da ke tura shanunsu cikin gonaki a yankin

An rahoto cewa shanu sama da 12 sun mutu biyo bayan bugun tsawa a garin Urhodo-Ovu na karamar hukumar Ethiope East na jihar Delta, The Nation ta ruwaito.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, makiyayan suna zaune kusa da shanun yayin da aka dauke wasu daga ciki zuwa wani yanki na daji don kiwo lokacin da tsawar ta fado kan shanu sha biyu.

Majiyar ta yi bayanin cewa tsawar ta fado wa shanun ne bayan an dan yi ruwan sama, inda ta kara da cewa 'yan mintoci kadan sai shanun suka fadi matattu saboda cikinsu ya kumbura.

KU KARANTA: Tabbatar da Tsaro a Bikin Sallah: An Jibge ’Yan Sanda Sama da 4000 a Jihar Kano

Bayan Ruwan Sama, Tsawa Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Shanu Sama da 12
Bayan Ruwan Sama, Tsawa Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Shanu Sama da 12 Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Majiyar ta bayyana cewa kashe shanun da tsawar ta yi ya sanya tsoro a zukatan makiyayan wadanda bayan faruwar lamarin suka tsere amma daga baya suka dawo.

An gano cewa kafin ranar da abin ya faru, manoma a lokuta da dama sun gargadi makiyayan da su daina tura shanunsu zuwa gonakin rogonsu amma ba su saurara ba har sai da lamarin ya faru.

Lamarin wanda ya jawo hankalin mutane daga kauyukan da ke makwabtaka da suka bayyana yadda suka ji sun ce har yanzu suna cikin kaduwa game da lamarin, sun kara da cewa wannan zai zama gargadi ga makiyayan da ke daukar shanunsu don lalata gonaki.

Dangane da jita-jitar da ake yadawa cewa lamarin na da alaka da bakin jama'a, wata majiyar ta ce irin wannan lamarin ya faru a wasu garuruwa, cewa wannan ba sabon abu bane.

KU KARANTA: Da Dumi-dumi: Gwamna Ya Kori Kwamishinoninsa har 20 cikin 28 Daga Aiki

A wani labarin, Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta ce tana adawa da biyan kudin fansa ga 'yan bidiga don ganin an sako mutanen da aka sace, TheCable ta ruwaito.

Kungiyar kolin ta zamantakewar al'ummar arewa, ta ce tana goyon bayan tattaunawa da 'yan bindigan.

Emmanuel Yawe, sakataren yada labarai na ACF na kasa, ya bayyana matsayin kungiyar a Kaduna ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel