Masallatan da Aka sace Daga masallacin Katsina Sun Samu Yanci

Masallatan da Aka sace Daga masallacin Katsina Sun Samu Yanci

- Rahoto ya nuna cewa mutane 11 cikin wadanda yan bindiga suka sace a masallacin Jibiya da ke jihar Katsina sun samu yanci

- Hakan ya kasance ne da taimakon matar daya daga cikin yan fashin da suka sace su, inda ta kwance su sannan ta nemi su tsere

- A yanzu dai saura mace daya a wajensu, sun kuma bukaci a biya miliyan 10 kafin su sake ta

Akalla mutane 11, ciki har da wani jariri, da aka sace daga masallacin Jibia da ke jihar Katsina ne suka sake samun ‘yanci.

An sace masu bautar ne a ranar Litinin a wani masallaci da ke bayan garin Jibiya na Jihar Katsina yayin da suke gudanar da sallar tahajjud.

KU KARANTA KUMA: Buhari Ya Ba Sarkin Musulmi da Sauran Shugabannin Addinai Sabon Aiki

Masallatan da Aka sace Daga masallacin Katsina Sun Samu Yanci
Masallatan da Aka sace Daga masallacin Katsina Sun Samu Yanci Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Wani mazaunin yankin, Fahad Mukhtar ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa wadanda lamarin ya rutsa da su sun tsere daga hannun wadanda suka sace su ne da yammacin Laraba a karamar hukumar Zurmi na jihar ta Zamfara da ke makwabtaka.

Kamar yadda wani ganau ya shaida, wata mata da ke auren daya daga cikin ‘yan fashin ne ta taimaka wajen kwancensu daga inda aka ajiye su sannan ta nemi su gudu.

Wadanda suka tsere sun hada da maza takwas da mata uku.

Mutum guda da aka bari ita ce wata mai jego wacce aka ceto danta amma ita bata iya tserewa ba saboda kafufunta sun kunbura kuma ta kasa gudu.

Yanzu haka masu garkuwan na neman kudin fansa miliyan N10 kafin su sake ta.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Daga karshe Gwamnan Najeriya ya magantu, yace ya san inda yan fashi ke da zama

Hukumomin 'yan sanda a jihar ba su tabbatar da faruwar lamarin ba saboda ba a dauki kiran wayar da aka yi wa kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isah ba.

A baya Legit.ng ta kawo cewa akalla mutane 40 ne ‘yan bindiga suka sace a yayin da suke gudanar da sallar Tahajjud a wani masallaci da ke garin Jibiya na jihar Katsina.

Mazauna garin sun shaida wa jaridar Daily Nigerian cewa ‘yan bindiga da dama sun kai hari a masallacin da misalin karfe 2 na daren Litinin kuma suka tafi da masu ibadar.

An tattaro cewa masu garkuwan da farko sun dauki mutane 47, ciki harda mata da yara, amma daga baya bakwai suka dawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng