Buhari Ya Ba Sarkin Musulmi da Sauran Shugabannin Addinai Sabon Aiki

Buhari Ya Ba Sarkin Musulmi da Sauran Shugabannin Addinai Sabon Aiki

- Shugaba Buhari ya nemi shugabannin addinai a kasar da su goyi bayan yaki da rashin tsaro

- Buhari ya gabatar da wannan bukatar ne a ranar Juma’a, 14 ga watan Mayu, yayin tattaunawa ta wayar tarho da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III

- Don haka, Sultan ya yi alkawarin ba da goyon baya ga ci gaba da kasancewar Najeriya

An nemi Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III da sauran shugabannin addinai a kasar nan da su hada kai waje guda don nuna goyon baya ga yaki da ta’addanci, satar mutane, fashi da makami da cutar COVID-19.

Jaridar PM News ta bada rahoton cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya gabatar da wannan bukatar a ranar Juma’a, 14 ga watan Mayu, a Abuja, babban birnin kasar.

KU KARANTA KUMA: IBB saurayina ne amma yanzu bama tare domin na rabu da shi, in ji Ummi Zee Zee

Buhari Ya Ba Sarkin Musulmi da Sauran Shugabannin Addinai Sabon Aiki
Buhari Ya Ba Sarkin Musulmi da Sauran Shugabannin Addinai Sabon Aiki Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa Malam Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shuaban kasa kan harkokin yada labarai, a cikin wata sanarwa ya ce Buhari ya yi kiran ne yayin tattaunawa ta wayar tarho da Sarkin Musulmi.

Rahoton ya ce Sultan ya yi kiran ne don taya Shugaban kasar murnar kammala azumin Ramadan cikin nasara da kuma gabatar da Sallar Idi.

Jaridar Sun ta kuma ruwaito cewa shugaban ya yi kira da a ci gaba da tattaunawa tsakanin shugabannin manyan addinan biyu domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali don yin mulki a kasar.

Ya yaba wa mai alfarma Sarkin Musulmi kan kyakkyawan shugabancin da ya ke yi wa al’ummar Musulmi kuma ya yaba masa da hadin kan da ake samu a karkashin sa.

Sultan a nasa bangaren ya yi alkawarin jajircewa ga ci gaba da kasancewar kasar a matsayin tsintsiya daya.

KU KARANTA KUMA: IBB yana nan da ransa cikin koshin lafiya, majiyoyi sun karyata rade-radin mutuwar tsohon Shugaban Najeriyan

Ya ba shugaban kasar tabbacin samun goyon bayan Masarautar a kokarin da take yi na maance matsalolin da kasar ke fuskanta.

A wani labarin, a tsaka da yanayin rashin tsaro a kasar, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya gano mutanen da ke da hannu a matsalolin tsaro a fadin arewa.

Jaridar Sun News ta ba da rahoton cewa Mohammed ya yi ikirarin cewa yawancin ayyukan ta'addanci na baya-bayan nan kamar su satar mutane, fashi da makami, da sauran su Musulmai ne ke ci gaba da aiwatar da su.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 13 ga watan Mayu, yayin da yake zantawa da manema labarai a masaukin shugaban kasa, Ramat House, Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel