Kurunkus: 'Yan bindiga sun bayyana masu basu makamai kuma suke raba kudin fansa

Kurunkus: 'Yan bindiga sun bayyana masu basu makamai kuma suke raba kudin fansa

- Miyagun 'yan bindiga sun bayyana cewa jami'an DSS da na 'yan sanda ne ke basu makamai suna mugun aiki

- Kamar yadda aka zanta dasu, sun ce suna raba kudin fansa ne da jami'an tsaron da ke basu makaman

- Tun dai a 2018, TY Danjuma ya sanar da cewa akwai jami'an tsaron da ke taimakawa ta'addanci a kasar nan

'Yan bindigan da suka dade suna addabar yankuna daban-daban na kasar nan sun ce suna samun makamai ne daga jami'an hukumar tsaro ta farin kaya kuma su kan raba kudin fansa tare ne idan sun karba.

'Yan ta'addan sun sanar da Deutsche Welle a wani rahoto da suka fitar na cewa suna aron makamai ne daga jami'an tsaro farin kaya kuma suna raba kudin da suka samu, Vanguard ta wallafa.

'Yan ta'addan sun kara da cewa wasu daga cikin jami'an 'yan sanda na daga cikin wadanda suke hada kai dasu wurin assasa wutar rashin tsaro a kasar nan wanda kuma ake zargin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasa shawo kai.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Sultan yayi muhimmin kira ga Shugaban Buhari da Gwamnoni

Kurunkus: 'Yan bindiga sun bayyana masu basu makamai kuma suke raba kudin fansa
Kurunkus: 'Yan bindiga sun bayyana masu basu makamai kuma suke raba kudin fansa. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Wani mai magana da yawun hukumar tsaro ta farin kaya ya ki yin tsokaci a kan lamarin.

Rahoton ya yadu a kafafen yada labarai a yayin da ake tsaka da yada jita-jita cewa jami'an tsaron kasar nan ne ke assasa wutar rashin tsaro kuma suke samun kudi.

A 2018, Theophilus Danjuma, tsohon shugaban sojin Najeriya yace rundunar sojin Najeriya da wasu jami'an tsaro ne ke samarwa 'yan ta'adda makamai domin su cigaba da aiwatar da ayyukan ta'adda a kasar nan.

Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta musanta wannan zargin amma alamu masu yawa suna cigaba da bayyana cewa akwai kamshin gaskiya.

A makon da ya gabata ne shugaba Buhari ya ja kunnen Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai inda 'yan bindiga suka kashe dubban jama'a, da ya rungumi tsarin Ruga ko kuma ya jure rigingimun jama'a.

A watan da ya gabata, Buhari ya tsaya tsayin daka kan Isa Pantami, daya daga cikin ministocinsa wanda ake zargi da nuna goyon baya ga ta'addanci

KU KARANTA: Da duminsa: Tsohon shugaban ma'aikatan tsaro na Najeriya ya rasu

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari yace mulkinsa zai yi amfani da duk wata dama da dabaru da ya sani wurin yin maganin 'yan bindiga domin tabbatar da samuwa abinci a damina mai zuwa.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, shugaban kasan ya sanar da hakan ne ga manema labarai na gidan gwamnati jim kadan bayan kammala sallar idi a ranar Alhamis.

Kamar yadda yace, matsalar 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane za a shawo kanta domin tabbatar da cewa kasar bata fada kalubalen rashin abinci ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel