Rashin tsaro: Sultan yayi muhimmin kira ga Shugaban Buhari da Gwamnoni

Rashin tsaro: Sultan yayi muhimmin kira ga Shugaban Buhari da Gwamnoni

- Sultan Alhaji Sa'ad Abubakar III, sarkin Musulmi, ya bukaci Buhari da gwamnoni da su kawo karshen rashin tsaro

- Kamar yadda shugaban majalisar koli ta al'amuran addinin Musulunci na kasa yace, Musulmi su cigaba da yi wa shugabannin addu'a

- Shugaban yace nauyin baiwa rayuka da jama'a kariya ya hau kan shugabanni, don haka dole ne su sauke shi

Sarkin Musulmi, Sultan Alhaji Sa'ad Abubakar III ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni da su kawo karshen rashin tsaro a kasar nan, Jaridar The Nation ta wallafa.

Sarkin Musulmin wanda shine shugaban majalisar koli ta al'amuran addinin Musulunci a Najeriya, yayi wannan jawabin ne a Sokoto bayan sallar idin karamar sallah da aka yi a ranar Alhamis da ta gabata.

Ya ce: "Muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da dukkan gwamnonin jihohi da su gaggauta kawo karshen rashin tsaro da ya addabi kasar nan.

KU KARANTA: Boko Haram: Majalisar tarayya ta bukaci duba ababen hawa da kyau kafin shigarsu ciki

Rashin tsaro: Sultan yayi muhimmin kira ga Shugaban Buhari da Gwamnoni
Rashin tsaro: Sultan yayi muhimmin kira ga Shugaban Buhari da Gwamnoni. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Haramta kiwo: Ndume yayi martani mai zafi ga Gwamnoni 17 na kudanci

"A matsayinku na shugabanni, dole ne ku dage wurin sauke nauyin dake kanku na bada kariya ga al'umma.

"A don haka, dole ne ku kare zagewa wurin ganin kun dawo da zaman lafiya a kasar nan irin wanda muka dade da sanin muna da shi."

Sarkin Musulmin yayi kira ga Musulmi da su cigaba da yi wa shugabanninsu addu'a domin Allah ya basu damar daukar dawainiyar da ta hau kansu.

Yayi kira ga Musulmi da su cigaba da bayyana halayyar karamci da kaunar juna wanda sallah ke nunawa.

"Yau babbar rana ce garemu ta murna, ku nuna osyayya, kauna, goyon baya kuma a yi mu'amala mai kyau."

A wani labari na daban, a kalla 'yan sanda hudu ne ke tsaron gidan Maikano Abdullahi, jami'in fadar shugaban kasa wanda wasu barayi suka yi yunkurin shiga gidansa.

An gano cewa jami'an tsaro biyu ke aiki a lokaci daya, rana biyu, dare biyu a gidan, jaridar The Punch ta ruwaito.

Gidan yana da kusanci da gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ke da kusancin mitoci kadan da wani wurin da sojoji hudu ke zama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng