Da Dumi-dumi: Shugaba Buhari Ya Amince da Sabbin Matakan Tsaro a Kudancin Najeriya

Da Dumi-dumi: Shugaba Buhari Ya Amince da Sabbin Matakan Tsaro a Kudancin Najeriya

- Shugaba Muhammadu Buhari ya aminci da sabbin matakan tsaro don magance rikici a kudanci

- Ya kuma amince da wata takarda kan batun shan muggan kwayoyi da aka gabatar a taron da aka yi

- An dauki kwanaki ana gudanar da tarurruka don samar da mafita ga matsalolin tsaron Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sabbin matakan tsaro ga yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu na kasar, The Nation ta ruwaito.

Wannan na daya daga cikin sakamakon jerin tarurrukan tsaro da aka gudanar a cikin kwanaki 11 da suka gabata kuma aka kammala a ranar Talata a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.

Mukaddashin Sufeto-janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar Gwamnatin bayan taron, amma, ya ki ba da cikakken bayani.

KU KARANTA: 'Yan Kasuwa Sun Tafka Asara Bayan Mummunar Gobara da Ta Yi Kaca-kaca da Kasuwa

Da Dumi-dumi: Shugaba Buhari ya Amince da Wasu Matakan Tsaro a Kudanci
Da Dumi-dumi: Shugaba Buhari ya Amince da Wasu Matakan Tsaro a Kudanci Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Shugaban ya kuma amince da wata takarda da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (rtd) ya gabatar, kan batun shan muggan kwayoyi, wadanda ya ce suna taimakawa Rashin tsaro, amma kuma bai yi karin bayani ba.

NSA ta ce taron ya jaddada bukatar magance matsalolin tsaro a kasar nan musamman wadanda suka taso a ‘yan watannin da suka gabata.

KU KARANTA: Saboda Ayaba, Wani Soja Ya Bindige Dan Kasuwa a Jihar Zamfara

A wani labarin, Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana firgici game da fashin da aka yi a kusa da fadar shugaban kasa, Aso Villa a babban birnin tarayya Abuja.

PDP ta nuna damuwa kan lamarin, tana mai zargin rashin iyawar shugaba Muhammadu ta fuskar bai wa kasar cikakken tsaro don kare rayukan al'umma.

A daren jiya Litinin ne fadar shugaban kasa ta fitar wata sanarwa ta hannun mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu cewa 'yan fashi sun afka gidan shugaban ma'aikata na shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; lamarin da ya jawo cece-kuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel