Yajin Aiki: Gwamnati Ta Amince da Daya Daga Cikin Bukatun Likitocin Najeriya

Yajin Aiki: Gwamnati Ta Amince da Daya Daga Cikin Bukatun Likitocin Najeriya

- Gwamnatin Buhari ta amince da tsawaita shekarun ritayar likitoci da ma'aikatan lafiya

- Hakazalika za a tattauna kan batun alawus na hadari a ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa

- Gwamnati ta bayyana amincewar a matsayin wata dabara ta rike likitocin a gida Najeriya

Gwamnatin Tarayya a ranar Talata ta amince da daya daga cikin bukatun ma'aikatan kiwon lafiya ta hanyar tsawaita shekarun ritaya zuwa shekaru 65.

Gwamnatin ta kuma amince da shekaru 70 a matsayin shekarun ritaya ga kwararrun likitoci, Daily Trust ta ruwaito.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya bayyana hakan ne a Abuja bayan ganawa tsakanin kwamitin Shugaban kasa kan albashi, da Kungiyoyin Kwararru na fannin Kiwon Lafiya da Kungiyoyin Kwadago kan batun Alawus na Hadari da kuma shekarun ritaya.

Da yake jawabi ga manema labarai daga baya, Ngige ya ce: “Mun karbi shawarwarinsu. Bangaren gwamnati za ta tsayar da nata shawarwarin kuma za mu sake haduwa a ranar 1 ga watan Yuni domin mu samu matsaya kan alawus na hadari ga ma’aikatan lafiya a Najeriya.

KU KARANTA: Karamar Sallah: An Jibge 'Yan Sanda 3200 a Imo Don Tabbatar da Tsaro

Yajin Aiki: Gwamnatin Ta Amince da Daya Daga Cikin Bukatun Likitocin Najeriya
Yajin Aiki: Gwamnatin Ta Amince da Daya Daga Cikin Bukatun Likitocin Najeriya Hoto: ripplesnigeria.com
Asali: UGC

“Mun kuma tattauna batun shekarun ritaya ga ma’aikatan kiwon lafiya, kasancewar muna son ci gaba da rike ma’aikatanmu na kiwon lafiya a nan Najeriya.

"Mutane da yawa suna zuwa nan don su yi saraf su kwace mutanen da muka horar da su da matukar tsada. Yana daukar kudi da yawa a horar da likita, nas ko masanin kimiyyar dakin gwaje-gwaje ko likitan kashi.

“Don haka, muna so mu rike su a nan. Za a iya rike su na dogon lokaci ta hanyar tsawaita shekarun ritayar su har zuwa 65 ga ma’aikatan lafiya na yau da kullun da likitoci, da kuma shekaru 70 ga kwararrun likitoci.’’

Shugaban, kungiyar likitocin Najeriya, Emmanuel Ujah da takwaransa na kungiyar hadin gwiwar sashin lafiya, Josiah Biobelemoye, sun bayyana kwarin gwiwar cewa za a cimma wata yarjejeniya da za ta iya bai wa ‘yan Najeriya ingantattun ayyukan kiwon lafiya.

KU KARANTA: Jerin Kasashen Da Basu Ga Wata Ba, Ba Kuma Za Su Yi Sallar Idi Gobe Laraba Ba

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sabbin matakan tsaro ga yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu na kasar, The Nation ta ruwaito.

Wannan na daya daga cikin sakamakon jerin tarurrukan tsaro da aka gudanar a cikin kwanaki 11 da suka gabata kuma aka kammala a ranar Talata a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.

Ikeokwu ya ce ‘yan sanda sun yi shiri yadda ya kamata don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a lokacin bikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel