'Yan Boko Haram 8 Cikin Waɗanda Suka Kai Hari Maiduguri Sun Baƙunci Lahira

'Yan Boko Haram 8 Cikin Waɗanda Suka Kai Hari Maiduguri Sun Baƙunci Lahira

- Yan sanda sun halaka yan ta'adda takwas da suka kawo hari a Maiduguri

- Yan ta'addan sun afka garin ne a yammacin Talata yayin da mutane ke shan ruwa

- Yan ta'addan na kan kona gidajen mutane ne kwatsam yan sandan suka far musu

Jami'an yan sanda sun halaka a kalla yan ta'addan Boko Haram takwas da suka yi yunkurin kai wa mazauna garin Maidguri, babban birnin jihar Borno hari a yammacin ranar Talata, PRNigeria ta ruwaito.

Legit.ng ta ruwaito cewa yan ta'addan sun shiga cikin garin da motocci masu bindiga da babura da dama a ranar Talata yayin da musulmi ke shirin yin bude bakin azumin Ramadan.

'Yan Sanda Sun Kashe 'Yan Boko Haram 8 Da Suka Kai Hari Maiduguri
'Yan Sanda Sun Kashe 'Yan Boko Haram 8 Da Suka Kai Hari Maiduguri. Hoto: @thecableng
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Rikicin Limanci: Gwamnati Ta Rufe Masallaci Bayan Limamai Biyu Sun Mutu a Osun

Wata majiyar sirri ta shaida wa PRNigeria cewa yan ta'addan suna cikin kona gidajen mutane ne a Jiddari Polo a yayin da yan sandan karkashin jagorancin CSP Mohammed Ibrahim suka iso unguwar da mota mai bindiga.

"Suna hango yan tawagar yan sandan, yan ta'addan sunyi yunkurin tserewa. A yayin da suke bin sahunsu, motar yan sandan ta bi ta kan wasu yan ta'addan ta kashe su nan take.

"Mun kirga a kalla gawarwaki takwas wasu kuma sun yi kaca-kaca. A halin yanzu da na ke magana da kai, gawarwakin na kwance a Jiddari Polo. Yau yan ta'addan sun sha kaye.

KU KARANTA: Za'a Yi Dokar Da Za Ta Bawa Mata Damar Auren Miji Fiye Da Ɗaya a Afirka Ta Kudu

"Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da bindigar harbo jirgin sama, AK-47 da mota mai bindiga," a cewar majiyar.

Daga bisani wata tawagar jam'ian tsaro da ta kunshi sojoji, yan sanda da Civilian JTF sun iso domin fatattakar yan ta'addan da ke tserewa.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel