Yan Sanda Sun Kama Manyan Masu Garkuwa da Mutane Su 6 a Abuja

Yan Sanda Sun Kama Manyan Masu Garkuwa da Mutane Su 6 a Abuja

- An kama wasu manyan masu garkuwa da mutane shidaa yankunan Gwagwalada da Kwali a babban birnin tarayyar Najeriya

- An ruwaito cewa an gano wuraren da ake ajiye mutanen da aka yi garkuwa da su

- Rundunar yan sanda ta kuma bayyana cewa har yanzu tana bin sawun sauran wadanda ake zargin

An kama wasu manyan masu garkuwa da mutane shida da ke da alhakin sace-sacen mutane a yankin Gwagwalada da Kwali a wani babban ci gaba da rundunar ‘yan sanda ta Babban Birnin Tarayya (FCT) ta samu.

PRNigeria ta tattaro cewa ‘yan sanda sun cafke wadanda ake zargin a wurare daban-daban bayan tattara bayanan sirri.

KU KARANTA KUMA: Yan Bindiga Sun Kashe Jami’in Dan Sanda a Wani Harin Bazata a Sokoto

Yan Sanda Sun Kama Manyan Masu Garkuwa da Mutane Su 6 a Abuja
Yan Sanda Sun Kama Manyan Masu Garkuwa da Mutane Su 6 a Abuja Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Wani babban jami'in da ke yaki da masu satar mutane ya fada wa jaridar cewa an kuma gano wuraren da ake tsare da wadanda aka yi garkuwa da su har sai an biya kudin fansa.

Ya ce: “Bayan gudanar da sa ido da tattara bayanan sirri, runduna ta musamman mai yaki da satar mutane ta rundunar ‘yan sanda ta samu nasarar cafke wasu mutane shida da ake zargi wadanda ke bayan manyan sace-sacen mutane ne a Tungan Maji da ke Gwagwalada da Kwaita a yankin Kwalli.

“An cafke su ne a wurare daban-daban bayan an binciko maboyar da suka saba ajiye wadanda suka yi garkuwar da su. Har yanzu muna bin sawun sauran wadanda ake zargin.”

KU KARANTA KUMA: Rundunar Soji da Yan Sanda Sun Sha Kan Yan Bindiga a Harin Masallaci a Katsina

A wani labarin, mayakan kungiyar Boko Haram sun cinna wuta a wasu a gidaje a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.

Ana kuma jin karar harbin bindiga da abubuwa masu fashewa a sassan birnin daban-daban musamman kusa da Jiddari Polo.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa ana musayar wuta tsakanin sojoji da wasu da ake zargin yan ta'adda ne a kusa da Molai da Jiddari a babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel