Rundunar Soji da Yan Sanda Sun Sha Kan Yan Bindiga a Harin Masallaci a Katsina

Rundunar Soji da Yan Sanda Sun Sha Kan Yan Bindiga a Harin Masallaci a Katsina

- Rundunar soji ta ce dakarunta da hadin gwiwar rundunar yan sandan kasar sun yi nasarar dakile harin yan bindiga a kan masallata

- Yan bindiga sun kai farmaki ne a babban Masallacin Magama da ke karamar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina a yayin sallar tahajjud

- Dakarun tsaron sun kuma yi nasarar ceto da yawa daga cikin mutanen da suka yi garkuwa da su, sun kuma sada su da yan uwansu

Rundunar sojojin Najeriya a ranar Talata ta ce dakarunta da kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya sun dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a babban Masallacin Magama da ke karamar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina.

Sojojin sun ce masu ibada a masallacin suna gudanar da Sallar dare na Ramadan lokacin da ‘yan bindigar suka afka wurin, suna harbi ba kakkautawa sannan kuma suka sace su.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa bayanin hakan ya fito ne daga bakin Daraktan hulda da jama'a na rundunar, Mohammed Yerima.

Rundunar Soji da Yan Sanda Sun Sha Kan Yan Bindiga a Harin Masallaci a Katsina
Rundunar Soji da Yan Sanda Sun Sha Kan Yan Bindiga a Harin Masallaci a Katsina Hoto: plustvafrica
Asali: UGC

Yerima ya ce an sha karfin 'yan ta'addan, wanda hakan ya sa aka kubutar da wadanda aka sace wadanda tuni aka sada su da iyalansu.

KU KARANTA KUMA: Da Duminsa: Ministan Abuja Ya Hana Zuwa Filin Idi a Bikin Karamar Sallah

Sanarwar ta ce: “Sojoji na dakarun 17 Brigade tare da hadin gwiwar jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya sun dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka yi shirin kai wa a babban Masallacin Magama da ke karamar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina inda mazauna yankin da dama suka tafi don yin sallar dare ta Ramadana.

“Lamarin, wanda ya faru da sanyin safiyar ranar 10 ga Mayu, 2021, ya ga dimbin 'yan fashi da suka zo suna ta harbi ba kakkaurawa a kokarin tarwatsa Sallar da sace bayin Allah wadanda ba su ji ba basu gani ba.

"An tilasta musu janyewa a cikin rudani yayin da suka hadu da karfin wuta daga wata tawaga hade da sojoji da jami'an' yan sanda wadanda aka tura garin cikin dabara biyo bayan bayanan Sirrin da aka samu a kan shiryayyen harin.

“Amma, yayin da sojojin suka ci gaba da yin taka tsantsan don dakile wani hari da za a kai wa masallacin,‘yan ta’addan da ke guduwa wadanda ba a san ainihin manufar su ba, yayin da suke ja da baya, sun yanke shawarar afkawa wani masallaci da ke wajen garin Jibia inda suka yi garkuwa da wasu mutane.

“Lokacin da suka samu labarin, sai hadaddiyar tawagar suka bi sawun‘ yan fashin, inda suka tilasta musu barin yawancin wadanda aka yi garkuwar da su yayin da suka gudu da wasu adadi da ba a sani ba.

“Wadanda aka kubutar din tuni suka hadu da danginsu yayin da ake ci gaba da kokarin ceto sauran tare da hadin gwiwar wasu rundunonin soji da ke makwabtaka da su ciki har da na Jamhuriyar Nijar.

KU KARANTA KUMA: Wani Ango Ya Wallafa Hotunan Kasaitaccen Bikin Aurensa, an Gano Amarya Sanye da Nikabi

"An shawarci mazauna yankin da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullun tare da kai rahoton duk wani abin da ba su sani ba ga jami'an tsaron da ke kusa da su."

A wani labarin, mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cikin ganawa da shugabannin tsaro na Najeriya a Fadar Shugaban kasa, Abuja.

Ganawar na zuwa ne sama da awanni 24 bayan wasu ‘yan fashi da makami sun yi yunkurin kai hari gidan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari.

Fadar Shugaban kasar ta sanar da batun ganawar ne ta shafinta na Twitter amma ba ta bayar da cikakken bayani kan ajandar ta ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel