Yan Bindiga Sun Kashe Jami’in Dan Sanda a Wani Harin Bazata a Sokoto

Yan Bindiga Sun Kashe Jami’in Dan Sanda a Wani Harin Bazata a Sokoto

- Wasu da ake zaton yan bindiga ne sun kashe akalla dan sanda guda a yankin Runjin Sambo da ke karamar hukumar Sokoto ta Kudu a jihar Sokoto

- Lamarin ya afku ne a daidai lokacin da maharan suka hango jami'an tsaron a yayinda suke sintiri a kusa da wani masallaci, sai suka bude masu wuta

- Sai dai ba a kama kowanne daga cikin yan bindigar ba domin sun tsere

'Yan bindiga sun kashe akalla dan sanda guda a yankin Runjin Sambo da ke karamar hukumar Sokoto ta Kudu a jihar Sokoto.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa an ga maharan wadanda suka kai kusan 20 a kan babura a kusa da harabar babban jami’ar Usmanu Danfodio da misalin karfe 1:45am na ranar Talata.

KU KARANTA KUMA: Da Duminsa: Ministan Abuja Ya Hana Zuwa Filin Idi a Bikin Karamar Sallah

Yan Bindiga Sun Kashe Jami’in Dan Sanda a Wani Harin Bazata a Sokoto
Yan Bindiga Sun Kashe Jami’in Dan Sanda a Wani Harin Bazata a Sokoto Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

An ruwaito cewa daga baya sun yi watsi da baburansu kuma suka taka da kafa kusa da wani masallaci da ke kusa da asibitin Noma a yankin inda dimbin musulmai suka taru don yin sallar tahajjud.

Bayanai daga yankin sun ce, motar ‘yan sanda da ke sintiri ta matsa kusa da inda lamarin ya faru yayin sintirin da suke yi na yau da kullun kuma da ‘yan fashin suka ga ’yan sanda sai suka bude wuta a kan motar sintirin sannan suka kashe dan sanda guda.

Mazauna yankin sun ce sauran ‘yan sanda da ke cikin tawagar sintirin sun bi ‘yan fashin tare da bude musu wuta, amma babu daya daga cikin ‘yan fashin da aka buge domin duk sun tsere.

KU KARANTA KUMA: Yan Bindiga na Buƙatar Tattaunawar Sulhu Da Malamai, Inji Tshohon Shugaban NHIS

A wani labarin, rundunar sojojin Najeriya a ranar Talata ta ce dakarunta da kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya sun dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a babban Masallacin Magama da ke karamar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina.

Sojojin sun ce masu ibada a masallacin suna gudanar da Sallar dare na Ramadan lokacin da ‘yan bindigar suka afka wurin, suna harbi ba kakkautawa sannan kuma suka sace su.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa bayanin hakan ya fito ne daga bakin Daraktan hulda da jama'a na rundunar, Mohammed Yerima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng