Rundunar Soji Ta Bayyana Matakin da Zata Ɗauka Kan Zargin da Ake Mata a Jihar Zamfara

Rundunar Soji Ta Bayyana Matakin da Zata Ɗauka Kan Zargin da Ake Mata a Jihar Zamfara

- Rundunar Sojin ƙasar nan ta bayyana matakin da zata ɗauka kan zargin da ake yiwa wani jami'inta na kisan wani mai siyar da kankana a jihar Zamfara

- Kakakin rundunar, Muhammed Yerima, yace tuni suka fara gudanar da bincike kan lamarin domin gano gaskiyar abinda ya faru

- Yerima yace an ɗauki duk wani mataki da yakamata domin gujewa faruwar makamancin haka nan gaba

Rundunar soji ta fara bincikar zargin da akewa ɗaya daga cikin jami'anta na kashe wani mai siyar da kankana a jihar Zamfara.

KARANTA ANAN: Kungiyar Inyamurai Ta Ɗau Zafi Bisa Zargin Jami’an Soji Na Shirya Mata Wata Maƙarkashiya

Mutumin da aka kashe ya rasa rayuwarsa ne daga tambayar sojan ya bashi kuɗin abinda ya siya.

Mai magana da yawun rundunar soji ta ƙasa, Muhammed Yerima, shine ya bayyana haka a ranar Talata.

Rundunar Soji Ta Bayyana Matakin da Zata Ɗauka Kan Zargin da Ake Mata a Jihar Zamfara
Rundunar Soji Ta Bayyana Matakin da Zata Ɗauka Kan Zargin da Ake Mata a Jihar Zamfara Hoto: today.ng
Asali: UGC

Mr. Yerima yace lamarin abun dana sani ne, ya ƙara da cewa sojin Najeriya na miƙa ta'aziyyarsu ga iyalan wanda aka kashe.

Yace kwamandan runduna ta 8 dake jihar, Usman Yusuf, ya riga da ya naɗa wasu mutane da zasu gudanar da bincike kan lamarin wanda ya laƙume rayuwar mutum ɗaya.

A jawabinsa yace har yanzun ana ta ƙoƙarin gano wane jami'i ne yayi wannan ɗanyen aiki.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ba Za’a Ga Watan Sallah Ba Sai Ranar Laraba, Inji Hukumar NASRDA

Kakakin rundunar sojin yace:

"Rundunar soji ba zata amince da duk wani mummunan aiki da jami'anta za suyi akan mutanen da aka tura su domin su kare rayuwarsu."

"Kuma da zaran mun gano jami'in da yayi wannan kisan, za mu gudanar da tsattsauran bincike akansa, matuƙar muka gano zargin da ake masa gaskiya ne, ba makawa sai ya fuskanci hukunci dai-dai da abinda ya aikata.

"Muna kira ga mutanen jihar Zamfara cewa komai yakoma yadda aka sanshi a yankin da lamarin ya faru, sannan kuma jami'an mu zasu cigaba da gudanar da ayyukansu kamar yadɗa kundin tsarin mulki ya umarce su."

Mr. Yerima ya kuma musanta rahoton dake cewa an ƙona motar aikin jami'an soji kamar yadda wasu ke yaɗawa.

A wani labarin kuma Wike Ya Bada Kyautar Miliyan N220m Ga iyalan Jami'an Yan Sanda 11 da Aka Kashe

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike , ya bada gudummuwar miliyan 20 ga kowane ɗaya daga cikin iyalan jami'an yan sanda 11.

Gwamnan, wanda ya sanar da haka yayin da yakai ziyarar ta'aziyya ga kwamishinan yan sandan jihar, Friday Eboka, a hedkwatar hukumar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel